Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-11 16:49:30    
Sarki Huizong na daular Song ta arewa ta zamanin gargajiyar kasar Sin

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun malam Nuraddeen Ibrahim Adam, mazaunin Chiromawa Quarters, jihar Kano, tarayyar Nijeriya. Malam Nuraddeen Ibrahim Adam, a cikin wasikar da ka turo mana kwanan baya, ka ce, "kasancewa ni tsohon aminin Sashen Hausa ne, wato tun shekarar 1990, ina da matukar son sanin tarihi da kuma al'adun kasar Sin na fiye da shekaru 5,000. Dangane da haka, ina son ku ba ni tarihin sarki Hui Zong mai matukar son yin zane-zanen halitta, a cikin shirinku na Amsoshin Wasikunku da kuke gabatar mana a duk ranar Jumma'a."

To, a gaishe ka, malam Nuraddeen, kuma mun gode maka da sauraronmu a kullum da kuma kawo mana tambaya game da tarihin kasar Sin. Yanzu bari mu dan kawo maka tarihin sarki Huizong na zamanin gargajiyar kasar Sin.

Sarki Huizong, wanda ake kiransa Zhao Ji, ya kasance sarki na takwas a tarihin daular Song ta arewa ta zamanin gargajiyar kasar Sin, wato a wajen shekarar 1082 zuwa ta 1135. Sarki Song Huizong mutum ne mai taurin kai a fannin siyasa, har ma ya zamanto sarki mafi muni a tarihin daular Song ta arewa. Ya yi shekaru 25 yana kan karagar mulki, daga karshe, daularsa ta lalace, kuma mahara sun kama shi sun azabtar da shi har ya mutu, kuma a lokacin, yana da shekaru 54 da haihuwa.

Amma duk da haka, Sarki Huizong ya nuna gwaninta da kwarewa sosai a fannin zane-zane da kuma fasahar rubutun hannu, har ma ya shahara a tarihi sabo da zane-zanensa da kuma rubutun hannunsa.


1 2