Mataimakin shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasar Faransa, Bernard Lapasset ya ce, kwmaitin wasannin Olympics na Faransa ya gamsu sosai da dakunan wasanni da aka gina domin wasannin Olympics na Beijing."Beijing ya yi kyau, na zagaya wasu wuraren birnin Beijing, kuma dakunan wasanni suna da girma. Na iya tabbatar da cewa, su dakunan wasanni masu kyau ne ga 'yan wasa. Bayan 'yan watanni, wasannin Olympics na Beijing zai kasance wani kasaitaccen biki."
A cikin 'yan shekarun baya, hukumar kula da wasannin Olympics na Beijing ya mayar da batun muhallin birnin da ke daukar nauyin gudanar da wasannin Olympics a wani muhimmin matsayi. Tun farkon fari, a lokacin da gwamnatin kasar Sin ke neman daukar nauyin gudanar da wasannin Olympics, ta yi alkawarin gudanar da wasannin Olympics da ke da muhalli mai kyau. A game da wannan, Mr.Jacques Rogge, shugaban hukumar kula da wasannin Olympics ta duniya ya bayyana cewa, a lokacin da take share fage ga wasannin Olympics, gwamnatin Sin ta yi kokari sosai a wajen kyautata muhalli, kuma tana iya tabbatar da ingancin muhallin birnin Beijing a lokacin wasannin Olympics. Ya ce,"A cikin shekaru 6 zuwa 8 da suke wuce, masana'antun kasar Sin sun bunkasa cikin sauri, wanda har ya haddasa matsalar gurbaccewar iska. Amma muna nuna yabo ga kyawawan matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka, wadanda ba ma kawai domin wasannin Olympics ba, har ma domin daidaita matsalar muhalli cikin dogon lokaci." (Lubabatu) 1 2
|