Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-10 18:43:31    
'Yan kungiyar kwamitocin wasannin Olympics na kasashen duniya sun nuna yabo ga yadda Sin ta cika alkawuranta wajen neman daukar nauyin gudanar da wasannin Olympics

cri

Jiya a nan birnin Beijing, aka rufe babban taro na 16 na kungiyar kwamitocin wasannin Olympics na kasashen duniya, kuma bisa ajandar taron, yau 10 ga wata, kungiyar kwamitocin kasashen duniya sun yi taro tare da kwamitin zartaswa na hukumar kula da wasannin Olympics ta duniya. Wakilinmu ya yi hira da wasu mahalartan taron, kuma sun nuna yabo ga yadda birnin Beijing ke share fage ga wasannin Olympics, kuma a ganinsu, Sin ta cika alkawuran da ta dauka a lokacin da take neman daukar nauyin gudanar da wasannin Olympics.

Kungiyar kwamitocin wasannin Olympics na duniya tana kunshe da kwamitocin wasannin Olympics daga kasashe da shiyyoyi 205, wadanda ke karkashin jagorancin hukumar kula da wasannin Olympics ta duniya. A kan kira babban taron kungiyar kwamitocin kasashen duniya a shekaru biyu biyu, kuma daga ran 7 zuwa 9 ga watan nan da muke ciki, an gudanar da taron a karo na 16 a nan birnin Beijing.

A yayin da yake hira da wakilinmu, shugaban kungiyar kwamitocin wasannin Olympics na duniya, Mario Vazquez Rana ya ce, an gudanar da kyawawan ayyuka wajen share fage ga wasannin Olympics, kuma kasar Sin baki daya na kokari wajen gudanar da wasannin Olympics mai kyau. Ya ce,"Yanzu muna ci gaba da kokari, kuma muna fatan wasannin Olympics da za a gudanar a shekarar da muke ciki a birnin Beijing zai kasance mafi kyau a tarihi. Yanzu mun kusan cimma wannan buri. Ko shakka babu, wasannin Olympics na Beijing za su kasance mafi kyau a tarihi."

Mr.Rana ya kuma bayyana cewa, dukan kwamitocin wasannin Olympics 205 na kasashen duniya na nuna cikakken goyon baya ga wasannin Olympics na Beijing, kuma dalilin wannan aminci da suke da shi shi ne sabo da yadda kwamitin wasannin Olympics na Beijing ke share fage ga wasannin. Dimbin jami'an kwamitocin wasannini Olympics na kasashen duniya sun ce, Sin ta cika alkawuran da ta dauka a lokacin da take neman gudanar da wasannin Olympics.


1 2