Game da shawarwarin da gwamnatin kasar Sin da Dalai Lama suke yi, Mr Sita ya ce,
'Muna bude kofar yin shawarwari ga Dalai Lama. Amma ya zama tilas ne Dalai Lama ya daina dukkan laifuffukan nuna karfin tuwo, ya daina dukkan ayyukan lalata gasar wasannin Olympics ta Beijing, ya daina dukkan ayyukan kawo baraka ga kasar Sin, wannan ya zama muhimmin tushe da ake yin shawarwari da shi.'
Shugaban gwamnatin jihar Tibet da ke da ikon tafiyar da harkokinta da kanta Mr Mr Qiangba Puncog ya ci gaba da cewa,
'A halin yanzu dai, an riga an maido da oda ga zaman rayuwar jama'a da kuma ayyukansu a birni Lhasa, 'yan makaranta sun riga sun fara karatunsu, yawancin kantuna sun riga sun bude kofa, haka kuma an riga an sake bude kofar fadar Potala da dakunan nune nune ga 'yan yawon shakatawa. Ana samar da isassun kayayyaki a kasuwanni, farashinsu kuma ya zauna da gindinsa.'(Danladi) 1 2
|