A ran 9 ga wata a birnin Beijing, shugaban jihar Tibet da ke da ikon tafiyar da harkokinta ta kasar Sin Mr Qiangba Puncog, da kuma mataimakin shugaban sashen kula da harkokin dunkulalliyar kungiyar gwagwarmaya ta kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin Mr Sita sun amsa tambayoyin da manema labaru na gida da na waje suka yi musu. Sun bayyana cewa, gwamnatin jihar Tibet ta kasar Sin ta shirya sosai, domin tabbatar da mika wutar yola ta gasar wasannin Olympics cikin ruwan sanyi, suna fatan rukunin Dalai Lama zai daina ayyukan nuna karfin tuwo da kawo baraka ga kasar Sin, gwamnatin kasar Sin ta bude kofar yin shawarwari ga Dalai Lama.
Bisa shirin da aka yi, an ce, a watan Mayu ne, wutar yola ta gasar wasannin Olympics za ta isa dutsen Mt Qomolangma, wanda ya fi tsawo a duk duniya, haka kuma za a mika wutar yola a watan Yuni a jihar Tibet. Mr Qiangba Puncog ya ce, jihar Tibet da ke da ikon tafiyar da harkokinta da kanta ta riga ta shirya sosai, domin tabbatar da mika wutar yola cikin ruwan sanyi, ya ce,
'Shirya gasar wasannin Olympics ya zama babban buri da al'ummar kasar Sin take da shi cikin shekaru dari. Mika wutar yola a jihar Tibet ya zama abin alheri da kuma nauyin da ke bisa wuyan jama'ar jihar Tibet, jama'ar Tibet suna nuna goyon baya game da haka.'
1 2
|