Manazarta sun bayyana cewa, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da rashin samun isasshen lokacin barci cikin dogon lokaci zai kara nauyin da ke kan zuciya, ta haka za a iya kara hadarin kamuwa da cututtukan zuciya da hauhawar jini.
A 'yan kwanakin nan da suka gabata, kwararru na asibitin Rascondes na birnin Santiago, babban birnin kasar Chile sun gudanar da bincike kan mutane 700 da suka kamu da cuttuttukan toshewar jijiyoyin jini na zuciya da na kwakwalwa, daga baya kuma sun gano cewa, mutane da yawansu ya kai kashi 10 bisa dari shekarunsu bai kai 40 da haihuwa ba, kuma a cikin shekara guda kafin su kamu da ciwon, sun gamu da al'amuran bakin ciki, kamar kisan aure da mutuwar iyalansu. Shi ya sa kwararru suka nuna cewa, wannan ya shaida cewa, bacin rai wani mihimmin dalili ne da ya haddasa cuttuttukan jijiyoyin jini na zuciya da na kwakwalwa. Sabo da haka kwararru sun jaddada cewa, kasancewa cikin farin ciki zai ba da taimako sosai wajen magance ciwon toshewar jijiyoyin jini na zuciya da na kwakwalwa.(Kande Gao) 1 2 3
|