Kwararru masu aikin likitanci na kasar Chile sun nuna cewa, game da mutanen da suka kamu da cuttuttukan jijiyoyin jini na zuciya da na kwakwalwa, kashi 90 cikin dari daga cikinsu ne ba su yin zaman rayuwa yadda ya kamata, kuma hanyar zaman rayuwa ta kiwon lafiya za ta taimaka wa yawancin mutane wajen kau da damuwarsu ta kamuwa da ciwon toshewar jijiyoyin jini na zuciya da na kwakwalwa.
A kwanan nan, wata jaridar kasar Chile ta ba da labarin cewa, ta gudanar da binciken kimiyya kan wannan matsala, an gano cewa, shan taba da karuwar yawan kitsen da ke taruwa a jijiya, wanda ke hana jini gudu su muhimman dalilai ne da suka haddasa toshewar jijiyoyin jini na zuciya da na kwakwalwa, haka kuma bacin rai zai kara hadarin kamuwa da cuttuttukan jijiyoyin jini na zuciya da na kwakwalwa. Sabo da haka, kiyaye yin zaman rayuwa ta hanyar kiwon lafiya da kuma faranta rai za su ba da taimako wajen magance irin ciwace-ciwacen.
1 2 3
|