Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-03 14:16:06    
An gama bikin mika wutar gasar wasannin Olimpic ta Beijing a birnin Alma-aty na kasar Khazakstan

cri

Mr. Dossymbetov, sakatare janar na kwamitin wasannin Olimpic na kasar Khazakstan shi ma ya yi jawabi a gun bikin murna, ya ce, "Yau wata rana ce mai alfahari sosai ga dukkaninmu, muna jin dadi sosai da samun damar mika wutar wasannin Olimpic. Muna nuna godiya ga masu shirya wasannin Olimpic na Beijing da su ba mu wannan sa'a! Gasar wasannin Olimpic za ta zama wani gagarumin biki, kuma za ta zama wani babban al'amari ga kasar Sin kuma ga duk duniya baki daya."

Cikin nasa jawabi kuma Mr. Tasmagambetov, shugaban birnin Alma-aty ya bayyana cewa, "Birnin Alma-aty ya nuna maraba da hannu bibbiyu ga zuwan wutar yola ta gasar wasannin Olimpic ta "2008 ta Beijing"! Jama'ar birnin su ma sun yi haka, kuma sun yi alfahari da samun damar mika wutar su da kansu. Suna fatan za a yin bikin mika wutar gasar wasannin Olimpic ta Beijing lami lafiya!"

Daga baya kuma 'yan wasan raye-raye da wake-wake na musamma na kasar Khazakstan sun nuna wasannin kade-kade da raye-raye masu ban sha'awa, sun yi haka ne domin bayyana farin cikinsu sabo da nasarar da aka samu wajen mika wutar.

Bayan da aka gama bikin murna, wutar gasar wasannin Olimpic za ta tashi daga birnin alma-aty a wannan rana da dare cikin jirgin sama na musamman domin zuwa birnin Istanbul na kasar Turkey. (Umaru)


1 2