Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-04-03 14:16:06    
An gama bikin mika wutar gasar wasannin Olimpic ta Beijing a birnin Alma-aty na kasar Khazakstan

cri

A ran 2 ga wata da yamma da karfe 5 da wani abu bisa agogon wurin, Mr. Ermakhan Ibraimov, mai daga wutar yola kuma shahararren dan wasan dambe na kasar Khazakstan ya daga wutar kuma ya isa babban filin Astana na birnin Alma-aty, da haka ne aka sa aya tare da nasara wajen bikin mika wutar gasar wasannin Olimpic ta Beijing a tasha ta farko da aka yi wannan biki a kasashen ketare. Jama'a masu sauraro, yanzu za mu kawo muku wani bayani da wakilinmu ya ruwaito mana daga kasar Khazakstan.

A wannan rana wajen karfe 6 da yamma, an yi gagarumin bikin murna a babban filin Astana da ke tsakiyar birnin Alma-aty. Mr. Jiang Xiaoyu, mataimakin shugaban zartaswa na kwamitin wasannin Olimpic na Beijing, da Mr. Timur Dossymbetov, sakatare janar na kwamitin wasannin Olimpic na kasar Khazakstan, da Mr. Imangali Tasmagambetov, shugaban birnin alma-aty sun yi jawabai bi da bi a gun bikin.

Cikin nasa jawabi Mr. Jiang Xiaoyu, mataimakin shugaban zartaswa na kwamitin wasannin Olimpic na Beijing ya yi jinjina sosai ga aikin mika wutar gasar wasannin Olimpic da aka yi a birnin Alma-aty, ya bayyana cewa, "Birnin Alma-aty ya zama tasha ta farko ke nan da ake yin "ziyara cikin zaman jituwa" wato bikin mika wutar gasar wasannin Olimpic ta Beijing a kasashen ketare, kyawawwan yanayin birnin Alma-aty da kwarewarsa wajen shirya wannan biki, da sha'awar da jama'ar Khazakstan ke nunawa ga wutar gasar Olimpic, da kuma kyakkyawan zumuncin da suke nunawa ga jama'ar Sin, sun ba mu alama mai kyau a zukatanmu. Shugaba Nursultan Nazarbayev shi da kansa ne ya halarci kuma ya shiga bikin mika wutar, wannan ya ba da babban goyon baya ga wasannin Olimpic."

1 2