An ce, sakamakon tarzomar, fararen hula da yawansu ya kai 18 sun mutu, a yayin da yawan gidajen jama'a da aka kone ya kai 120. Sa'an nan, akwai kantuna 908 da aka cinna musu wuta tare da kwashe kayayyakinsu, tare da makarantu 7 da asibitoci 5 da suka lalace. Yawan hasarorin da aka sha a fannin tattalin arziki kai tsaye ya kai kudin Sin yuan miliyan 250. Losang, wani mazaunin birnin Lhasa ya fusata kwarai da gaske kuma ya ce,"na ji fushi sosai dangane da tarzomar da 'yan tsirarrun 'yan tawaye suka tayar kwanan baya a birnin Lhasa. Kwanciyar hankali da ci gaba da aka samu a Tibet nasarori ne da jama'a 'yan kabilu daban daban suka cimma bisa kokarinsu, kuma shi abu ne da ba da sauki ba aka samu. Amma ga su 'yan tawaye sun kawo mana manyan hasarori a cikin 'yan kwanaki kawai. A matsayinmu na mazaunan birnin Lhasa, muna jin fushi sosai. Bisa makarkashiyar rukunin Dalai Lama, sun aikata wa jama'a manyan laifuffuka, ko kadan ba za mu amince da makircinsu ba.
Dukar Tsering, wani masani a cibiyar nazarin al'adun Tibet ta kasar Sin, wanda ya dade yana nazari kan batun addini, ya ce, tun da can, gwamnatin kasar Sin na mai da hankali na musamman a kan addinin Buddah a Tibet, har ma ta zuba makudan kudade wajen gyara da kiyaye fadar Potala da wuraren ibada, ciki kuwa har da Tashilhunpo da Jokhang. A sa'i daya, gwamnatin kasar Sin tana kuma nuna kulawa ga zaman rayuwar sufaye, kuma sannu a hankali ne take sanya su cikin tsarin ba da kariya ga zaman al'umma. Ya ce,"binciken da na yi ya shaida cewa, su mabiyan Dalai Lama daidai sun kasance wadanda ke hana ruwa gudu wajen kafa daidaitaccen tsarin addinin Buddah na Tibet da maido da al'adun gargajiya na Tibet da ba da ilmi ga 'yan kabilar Tibet da tabbatar da kwanciyar hankali a Tibet."
Bayan aukuwar tarzomar, nan da nan hukumar jihar Tibet mai cin gashin kanta ta dauki matakai, don hukunta masu laifi bisa doka. yanzu kantuna da makarantu na gudana yadda ya kamata, kuma an maido da kwanciyar hankali a birnin Lhasa.(Lubabatu) 1 2
|