Saurari
Tarzomar da ta auku a tsakiyar watan nan da muke ciki a birnin Lhasa, hedkwatar jihar Tibet mai cin gashin kanta, ta jawo suka sosai daga wajen bangaren addini da mazaunan wurin da masana da dai sauran bangarori daban daban. Bi da bi ne suka bayyana cewa, tarzomar da masu laifi suka tayar ta saba wa manufar jin kai, haka kuma ta lalata nasarorin da ba da sauki ne aka samu ba wajen bunkasa birnin Lhasa. Sun kuma yi kira da a magance karin aukuwar al'amarin, don kwantar da hankulan jama'a.
A ranar 14 ga watan nan da muke ciki, wasu sufaye sun jefa duwatsu ga 'yan sanda wadanda ke aiki, daga baya, wasu 'yan tawaye sun fara taruwa a kan titi, suna kiran ballewar kasa, kuma suna ta dukan jama'a da farfasa abubuwa da kwashe kayayyaki da cinnawa gine-gine da motoci wuta, kuma tarzomar ta yadu cikin sauri, wadda ta lalata rayukan jama'ar wurin da dukiyoyinsu.
Drukhang Thubten Khedrup, shugaban reshen kungiyar addinin Buddah ta kasar Sin a Tibet ya ce, "na ga wasu sufaye suna sanya tufafin ibada, amma suna ta dukan jama'a da farfasa abubuwa da kwashe kayayyaki da cinnawa gine-gine da motoci wuta tare da wasu 'yan tawaye, ban da mamaki, na kuma ji kunya sosai. Aikinsu ya saba wa manufar jin kai, kuma bai dace da ka'idojin addinin Buddah ba. a matsayin mabiyan addinin Buddah, kamata ya yi mu kara gyara kanmu. kowa ya sani, yanzu jama'ar Tibet na zaman rayuwa cikin jin dadi, kuma al'adun addinin Buddah sun bunkasa sosai. Ina fatan gwamnati za ta hukunta masu laifi yadda ya kamata."
1 2
|