A ran 19 ga wata, shafin yanar gizo na Australia ya bayar da wani dogon bayani mai lakabi haka, "masu yawon shakatawa sun ga yadda aka da da kashi wa mutanen kabilar Han". A cikin wannan bayani, an ce, wasu masu yawon shakatawa na kasashen yammacin duniya wadanda suka bar tsaunin Himalayas sun bayyana cewa, a ranar da aka ta da zaune tsaye a birnin Lhasa, matasan Tibet mahaukata sun yi ta jifar 'yan kabilar Han da duwatsu, tare da yi wa 'yan kabilar Han duka, kuma sun kone shagunansu.
A ran 18 ga wata, Mr. Ken Wood, wani dan kasar Canada da sauran masu yawon shakatawa wadanda suka dauki jirgin sama suka isa birnin Kathmandu na kasar Nepal sun ga yadda aka ta da zaune tsaye a ranar Jumma'a, wato ran 14 ga watan Maris da idanunsu. Mr. Ken Wood ya ce, "Wannan matsala ce mai tsanani da aka shirya wa 'yan kabilar Han da musulmai". Wannan matsala ce ta nuna karfin tuwo da ta shafi birnin Lhasa gaba daya.
Wadannan masu yawon shakatawa na kasashen yammacin duniya sun almanta cewa, 'yan ta'adda sun yi duka wa 'yan kabilar Han da hannayensu da kafafunsu gaba daya ba tare da tausayi ko kadan ba. 'Yan Tibet sun zargi wadannan 'yan kabilar Han wadanda suka shiga yankin Tibet da cewa suna canja al'adun musamman na Tibet da hanyar zaman rayuwarsu. Mr. Ken Wood ya ce, ya ga wasu 'yan Tibet suna dukan wani dan kabilar Han wanda ke kan babur da duwatsu da kafafunsu. "Daga karshe dai sun duke shi sanda ya kwanta a kasa, sannan suka duke shi a kansa da duwatsu har ya rasa, kuma bai ko motsa ba."
Mr. Ken Wood ya ce, "ina tsammani wannan saurayi dan kabilar Han ya mutu." Amma jim kadan, Mr. Ken Wood ya kara da cewa, bai iya tabbatar da wannan ba. Amma Ken Wood ya tabbatar da cewa, bai ga wani dan Tibet da ya mutu a birnin Lhasa a cikin wannan matsala ba.
Shafin yanar gizo na Australiya ya nuna cewa, a ran 18 ga wata, wai gwamnatin Tibet wadda ke gudun hijira ta tabbatar da cewa, a cikin hargitsin da aka yi har na tsawon fiye da mako daya, 'yan Tibet 99 sun mutu sabo da duka da aka musu. Amma gwamnatin kasar Sin ta jaddada cewa, fararen hula 13 ne suka mutu sakamakon wannan hargitsi. Kuma lokacin da take kwantar da kura a Lhasa, ba ta yi amfani da kowane irin makamin da zai iya kashe mutum ba.
1 2
|