Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-20 13:52:27    
Koke-koken fararen hula na kasar Iraq

cri

Hanyar da Mr. Walid ya bi ta ba da wani misali ga wahalolin da fararen hula na kasar Iraq suka sha cikin shekaru 5 da suka wuce. Cikin wadannan shekaru 5 da suka gabata, an yi ta samun fashewar bomabomai da hare-hare da aikace-aikacen ta'addanci, da sabani tsakanin magoya bayan addinai a wannan yanki inda aka haifar da wayewar kai ta manyan koguna 2, kuma ana nan ana ta jawo lalacewa ga tarihi da al'adun Babylon wadanda suka yi shekaru 1000 da kafuwarsu. Mr. Audday Al-Katib ya tausaya sosai a wannan fanni ya ce, "Kasancewar sojojin Amurka a kasar Iraq ta zama matsala mafi muhimmanci ga kasar, kuma ta kara tsananta halin da ake ciki a Iraq. Harin da sojojin Amurka ke yi ya mai da Iraq ta zama filin yaki a tsakanin sojojin Amurka da dakaru masu yin adawa da su, sabo da haka an lalata biranen kasar sosai. Danyen aikin da Amurka ke yi wajen sa hannu cikin harkokin Iraq ya haddasa sabanin da ke tsakanin rukunonin addinan kasar, kuma ya haddasa mummunan tashin hankali a kasar. Ban da wannan kuma sojojin Amurka sun ta da hargitsin makamai kai tsaye, idan sojojin Amurka da kamfanin tsaro na kasar suka gamu da hadari, sai su yi amfani karfin makamai, har ma sun bude wuta kan fararen hula."

Danyen aikin da sojojin Amurka ke yi ya fusata mutanen Iraq kwarai, Mr. Al-Katib ya yi fushi da cewa, "Dole ne sojojin Amurka su fita daga Iraq! Iraq ba ta bukatar mamayewa! Sojojin Amurka da ke Iraq su ne sojoji 'yan kaka-gida. (Umaru)


1 2