Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-20 13:52:27    
Koke-koken fararen hula na kasar Iraq

cri

A ran 20 ga watan Maris yau da shekaru 5 da suka wuce, bisa karar jiniya da aka ji a sararin sama na birnin Baghdaza, hedkwatar kasar Iraq, sojojin kasar Amurka sun fara yin yaki a kasar Iraq. Bayan shekaru 5 da suka wuce wato a yau, yakin nan da Amurka ke masa jagora ba a kawo karshensa ba tukuna, amma bamban da haka ya kara nutsar da kasar Iraq cikin halin kaka-ni-ka-yi, kuma ya kara fitar da matsaloli da yawa. Cikin shekaru 5 da suka wuce, wadanne irin wahalolin da mutanen Iraq suka sha? Kuma ina ne mafitarsu? To, jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta muku wani bayanin da wakilinmu ya ruwaito mana mai cewa, Koke-koken fararen hula na kasar Iraq.

A ran 19 ga watan Maris na shekarar 2003, wato a gabannin yakin da aka tayar, Mr. Ali Walid ya yi fadi-tashi ya tashi daga Iraq tare da iyalinsa, kuma sun yi gudun hijira zuwa kasar Hadaddiyar daular Larabawa. Ya bayyana cewa, "Da ma iyalina yana da wani babban daki, bayan barkewar yakin, Amurkawa sun rushe kofar gidana, sun shiga ciki, yanzu babu kome a gidana. Ba na son Iraq ta da, kuma ba na son Iraq ta yanzu. A da Saddam Hussein ya jawo mana illa, amma yaya yanzu? Har ila yau muna shan wahala. Ko akwai bambanci wajen halin da muke ciki yanzu da na da? Akwai mana, wato halin da muke ciki sai kara lalacewa yake."

Cikin shekaru 5 da suka wuce bayan barkewar yakin, Mr. Walid ya taba komawa birnin Baghdaza sau 3, amma halin da ake ciki a can ba na a zo a gani ba ne, sabo da haka yana jin fushi da bacin rai. Ya ce, "Ba da dadewa ba bayan tashin yakin, na koma Iraq a karo na farko, a wancan lokaci kuwa na sa ran samun haske ga kasar Iraq. Amma bayan shekara daya, na koma Iraq a karo na 2, halin da ake ciki a lokacin ya wuce tsammani wato ya kara lalacewa. Bayan dawowata daga Iraq a karo na 3 kuma, na gaya wa 'yan iyalina cewa, sai ku manta da Iraq, ta lalace gaba daya."

1 2