Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-19 18:05:27    
Sabuwar hanyar da manoma da makiyaya na lardin Qinghai suke bi don kara samun wadata

cri

Wani malami mai suna Caigongtai da ke da shekaru 24 da haihuwa shi ma ya zuwa wurin nan daga makiyayar da ke jihar manyan tsaunuka , a gaban samarin da suka zo daga garinsa, ya waiwayi tarihinsa na koyon fasahar raye-raye, ya gaya musu cewa, a wancan shekaru, shi kansa ya bari garinsa zuwa babban birnin, ya yi aiki wurjanjan cikin mawuyacin hali kuma ya dogara bisa karfinsa na kansa, ya ce, wadannan samari sun sami sa'a in an kwatanta halin da suke ciki da nasa, ya ce, gwamnati ta samar musu sharuda masu kyau wajen karatu. Kullum Malam Caigongtai yana himmantar da dalibansa cewa, bayan karatu, kada ku koma gidajenku, ya kamata kuna ci gaba da nuna wasannin raye-raye , kada ku ja da baya, ku tafi zuwa birnin Beijing, ku hau dakalin nuna wasanni na Beijing, sa'anan kuma yana fatan za su iya tinkari zuwa dakalin nuna wasanni na duniya, kodayake hanyar nan na da wuya sosai, amma bai kamata ba ku ji tsoro, ku shawo kan matsalolin nan da imaninku, a karshe dai za ku iya cim ma burinku tare da nasara.

Bisa himmar malamin, daliban da ke karatu a kos din suna sa ran alheri ga makomar zaman rayuwarsu ta nan gaba, wata budurwar kabilar Tibet da ta zo daga wurin da ke dab da tsaunin Tangula mai suna Qimaocuo ta gaya wa manema labaru cewa, na yi mafarkin nuna wasannin raye-raye ga kowane mutum a dakalin duniya, ina son gaya wa aminanmu abubuwan da na ji na gani a lokacin da nake koyon fasahar nuna wasannin raye-raye, ina fatan aminanmu na kabilar Tibet za su nuna wasanninsu a sauran wurare bayan karatunsu duk domin sauyawar zaman rayuwarsu.

Bayan da malam Caigongtai ya ga ci gaban da dalibansa suka samu, sai yana ci gaba da fatansa na kara jan jagorar daliban zuwa babban matsayin nuna wasannin raye-raye na gargajiyar al'ummarsu. Ya bayyana cewa, bayan koyon fasahar nuna wasannin raye-raye a nan, ana iya tafi zuwa sauran wurare na duniya tare da raye-rayen garinsu, kuma za su iya samun kudin shiga don rage nauyin da ke bisa wuyan mutanen iyalansu, muhimmin abu shi ne, su farfugandar al'adun kabilunsu a kasashen waje, za a kara fahimtar kabilarmu Tibet, ta hakan za mu kara alfahari da al'ummarmu.

yanzu, ban da kudin shiga da aka samu daga wajen nuna wasannin raye-raye da kide-kide na gargajiyar kabilu daban daban, sai gwamnatin lardin Qinghai ta ba da goyon baya da gatanci ga manoma da makiyaya don kara musu kudin shiga ta hanyar yin zane-zane da sassaka mutum mutumi da yi wa riguna yawan dinki da yanka takardu ta hanyar yin amfani da armakashi da sauransu. Shugaban hukumar al'adu ta lardin Qinghai malama Cao Ping ta bayyana cewa, a kowace shekara, gwamnati ta shirya dandalin yin nunin kayayyakin da manoma da makiyaya suka yi. A lokacin nunin, gwamnati ta samar da karin kudi gare su wajen cin abinci da samun wurin kwana da zirga-zirga.

Bisa goyon baya da gwamnatin lardin Qinghai ta yi, ayyukan al'adun lardin sun sami bunkasuwa da sauri, kuma irin bunkasuwa ta kara wa manoma da makiyaya kudin shiga da yawa, mataimakin shugaban lardin Mr Ji Di Ma Jia ya bayyana cewa, ta hanyar raya ayyukan al'adu, ana gadon al'adun gargajiyar kabilunmu daban daban, a sa'I daya kuma, manoma da makiyaya su ma su iya kara samun kudin shiga, za su taka muhimmiyar rawa a lokacin da lardinmu ya raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma.(Halima)


1 2