Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-19 18:05:27    
Sabuwar hanyar da manoma da makiyaya na lardin Qinghai suke bi don kara samun wadata

cri

Jama'a masu sauraro, aikin horar da samarin da suka zo daga makiyayai a wani dakin horar da masu raye-raye na birnin Xining na lardin Qinghai da ke arewacin kasar Sin yana daya daga cikin matakan da gwamnatin lardin Qinghai ta dauka don kara kudin shiga ga makiyaya wadanda suka riga suka rasa kudin shiga bisa sanadiyar dakatar da kiwon dabbobi a makiyayai don mayar da ciyayi da za su kara tsawo kwarai , wato ana himmantar da makiyaya wajen yin amfani da fifikonsu na kwarewar raye-raye don nuna wasanninsu a wuraren yawon shakatawa don cim ma burinsu na kara samun kudin shiga.

Lardin Qinghai lardi ne da kabilu da yawa suke zama a cunkushe, yana da wadatattun albarkatun al'adun kabilu daban daban. A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, lardin Qinghai ya yi amfani da al'adun gargajiya na kabilu daban daban don kara samun kudin shiga ga makiyaya, kuma ya sami sakamako mai kyau, kungiyar raye-raye da kide-kide ta kabilu daban daban ta gundumar Ping'an ita ma tana daya daga cikinsu.

Mataimakin direktan sashen farfoganda na gundumar Ping'an Mr Wang Xuande ya yi amfani da rancen kudi yaun dubu 8 da ya samu daga banki ya kafa wata kungiyar nuna wasannin raye-raye da kide-kide na kabilu daban daban . A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, yawan mambobin kungiyar ya kara karuwa daga mutane 66 zuwa 520, kuma sun sa kafarsu a ko'ina a kasar Sin. Yanzu, kudaden shiga da 'yan kungiyar suka samu sun fi na sauran mutanen kauyensu yawa da ninki fiye da goma. Lokacin da Mr Wang Xuande ya waiwayi godiya da 'yanuwansa na kauyen suka yi masa, sai ya yi farin ciki da cewa, bayan da 'yan kungiyarmu suka nuna wasanni a cikin wasu kwanaki a wuraren da ke waje da kauyenmu, sai suka koma gida tare da kudin da suka samu da yawansu ya kai kudin Sin Yuan dubu 12 ko fiye, sun yi farin ciki sosai, mutanen iyalansu su ma sun bayyana cewa, abin nan na da kyau sosai . Kara samun kudin shiga ta hanyar al'adu ya sa 'ya'yanmu su sami moriya ta hakika, mun yi alfahari da wannan.

Bisa bukatun da hukumar al'adu ta lardin ta yi, an bayyana cewa, , wadanda suka zo kos din nan don neman koyon fasahar raye-raye a kalla za su iya nuna wasanni goma a cikin wata daya. Kodayake wadannan samari da suka zo daga makiyayai suna da abubuwan da suke da su ba tare da horon da aka yi musu ba, amma a cikin gajeren lokacin nan, dole ne su iya nuna wasanni da yawansu kamar hakan, amma abin wuya ne ga 'yan wasan raye-raye na musamman, balle a ce gare su. Yaya za a daidaita matsalar, malama Bao Guihua yar kabilar Mongoliya wadda ke da tarihin shekaru fiye da goma wajen koyar wa dalibai fasahar raye-raye ta gaya wa manema labaru cewa, a takaice dai, ba sauran hanya da za mu bi sai koyar da fasahar raye-raye ta hannu da hannu kai tsaye. In mun gano dan ci gaban da aka samu, to za mu nuna yabo sosai don kara musu imani.

1 2