Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-18 16:39:41    
Bunkasuwar makarantun koyar da harshen Larabci na gundumar Tongxin ta jihar Ningxia

cri

Makarantar koyar da Larabci ta Yuhai tana daya daga cikinsu, wadda aka kafa ta a shekarar da ta gabata. Kuma shugaban makarantar Hei Xinmin ya gaya mana cewa, "Dimbin gidaje na wurin suna fama da talauci sosai, ba su da abinci, har ma ba su da ruwan sha. Amma idan suna son fitar da kansu daga talauci, dole ne a samu ilmi da fasaha. Ganin haka, iyaye masu yawa sun tsai da kudurin tura yaransu cikin makarantun koyar da Larabci. Ta haka za su iya samun kudade da yawa, kuma za su canja zaman rayuwarsu kwata kwata."

Li Xiaohu wani dalibi ne da ke cikin makarantar, kuma ya gaya mana cewa, "dalilin da ya sa na zo makarantar shi ne sabo da yanzu Sin da kasashen Larabawa suna ta kara yin cudanya tsakaninsu, ana bukatar masu aikin fassara da Larabci da yawa, shi ya sa na zo makarantar domin koyon harshen, daga baya kuma zan iya zuwa birane masu ci gaba na kasar Sin domin cin rani."

Ban da harshen Larabci, makarantar ta koyar da ilmin cinikayya da na Kwamfuta da na Turanci, ta yadda dalibai za su iya cancantar ayyukansu cikin sauri bayan da suka gama karantunsu daga makarantar.

Ya zuwa yanzu, mutane fiye da 2500 da suka zo daga gundumar Tongxin suna gudanar da ayyuka da ke da nasaba da harshen Larabci a birane daban daban na kasar Sin har ma da na kasashen Larabawa.

To, masu sauraro, shirinmu na yau na "Musulmi na jihar Ningxia a ganin Kande" ke nan, muna fatan kun ji dadin wannan shirin musamman. Kande ta shirya muku wannan shiri a jihar Ningxia, kuma ke cewa a kasance lafiya. (Kande Gao)


1 2