Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-18 16:39:41    
Bunkasuwar makarantun koyar da harshen Larabci na gundumar Tongxin ta jihar Ningxia

cri

Yawan 'Yan kabilar Hui ya kai kashi 47 cikin dari na dukkan yawan mutanen birnin Wuzhong da ke tsakiyar jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kai ta kasar Sin. Har kullum fararen hula na kabilar Hui suna da al'adar shigad da yaransu cikin masallatai da makarantun koyar da harshen Larabci domin koyon Alkur'ani mai girma da kuma harshen Larabci. Tare da ingantuwar cudanyar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen da ke shiyyar gabas ta tsakiya, ana ta bukatar mutane da suka iya harshen Larabci, sabo da haka aikin fassara da Larabci ya zama wata sabuwar hanya ce ga dimbin 'yan ci rani ta kabilar Hui, kuma makarantun koyar da harshen Larabci sun samu bunkasuwa sosai.

Makarantar koyar da harshen Larabci ta gundumar Tongxin ta jihar Ningxia ita ce makarantar koyar da ilmin sana'a daya tak a kasar Sin wajen koyar da Larabci, wadda aka kafa ta a shekara ta 1985. kuma an kashe kudi kusan dala dubu 800 da bankin raya kasashen musulunci na duniya ya kebe.

Kuma ya zuwa yanzu, dalibai masu koyon harshen Larabci 500 sun riga sun gama karantunsu daga makarantar, kuma 30 daga cikinsu sun taba zuwa kasashen Saudi Arabia da Sudan da Masar da Libya da dai sauransu domin gudanar da aikin fassara da kuma kara ilminsu, yawancin sauran wadannan dalibai suna aiki a biranen Yiwu da Shenzhen da Beijing da Guangzhou inda aka fi samun 'yan kasuwa Larabawa da yawa. Shugaban makarantar Bai Shengyun ya bayyana cewa, "Aikin horar da masu aikin fassara da Larabci yana da ma'ana sosai, a fannin siyasa, ta kara ingantuwar dangantakar da ke tsakanin Sin da kasashen Larabawa, kuma a fannin tattalin arziki, ba kawai masu aikin fassara da Larabci sun samu dimbin kudade ba, har ma sauran mutane sun samu wannan hanyar samun kudi ta tallafawar da suka bayar."

Ganin babbar bukatar da aka yi wa masu aikin fassara da Larabci, gwamnatin gundumar Tongxin ta tsai da kudurin kara karfafa raya makarantun koyar da Larabci. Sabo da haka a 'yan shekarun nan da suka gabata, an kafa makarantu 6 masu zaman kansu, kuma yanzu ana iya horar da dalibai masu koyon harshen Larabci kusan 1000 a ko wace shekara.

1 2