Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-18 16:29:47    
Wurin yawon shakatawa na wasan Olympic a kan ruwa

cri

Fadin gine-ginen din din din a cikin wurin yawon shakatawa na wasan Olympic a kan ruwa ya kai misalin murabba'in mita dubu 18, sa'an nan kuma, fadin gine-ginen wucin gadi ya kai misalin murabba'in mita dubu 14. Fadin ruwan ya kai misalin murabba'in mita dubu 550. Bayan da aka cika hanyoyin gasa da ruwa, to, zurfin ruwan ya kai misalin mita 3.5, girman ruwan ya kai misalin cubic-metres miliyan 1 da dubu 700.

Babu tantama tilas ne a tabbatar da ingancin hanyoyin gasa, in aka haka irin hanyoyin gasa masu zurfi. Aiki mafi muhimmanci shi ne dole ne a aza harshi mai inganci, a hana ruwan ya shiga kasa. Kwararru sun sha yin dabara domin kammala wannan aiki.

Bayan da aka jarraba su ta hanyar cika su da ruwa, an sami kyakkyawan sakamako a fannin ingancin hanyoyin gasa. A watan Agusta na shekarar bara, an yi gasar fid da gwani ta tseren kwale-kwale ta matasa ta kasa da kasa a wurin yawon shakatawa na wasan Olympic a kan ruwa a Shunyi. Dukan bangarorin da abin ya shafa sun gamsu da wannan filin wasa sosai.


1 2