
Ya zuwa yanzu, bisa yarjejeniyar da aka daddale, babban kamfanin kera jiragen sama na Harbin Embraer ya riga ya samar da kimanin jiragen sama 20 ga kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama na kasar Sin daban daban. Malam Roberto Rossi de Souza ya gamsar da irin wannan kyakkyawan sakamakon da aka samu, kuma yana sa ran alheri ga makomar hadin gwiwar kasar Sin da ta Brazil a fannin kera jiragen sama. Ya ce, "mun sami kyakkyawan sakamako wajen yin hadin gwiwarmu. Muna gudanar da dukkan harkokinmu kamar yadda ya kamata. A ganinmu, wani abun da ya fito fili sosai shi ne, muna da kyakkyawar makomarmu bisa jiragen sama masu dimbin yawa da ake bukata a manyan kasuwannin kasar Sin da bunkasuwar da kasar ke samu cikin sauri. Sa'an nan kuma muna ganin cewa, mun sami abokiyar hadin gwiwarmu daidai. "

Ya zuwa yanzu, Malam Roberto Rossi de Souza ya riga ya shafe shekaru biyu yana zama a birnin Harbin. Da ya tabo magana a kan birnin, sai ya yi farin ciki da cewa, ko da yake ya zo kasar Sin ne daga kasar Brazil mai zafi, amma yanzu ba ma kawai ya riga ya saba da zamansa a birnin Harbin mai sanya da ke a arewacin kasar Sin ba, har ma yana kaunar wannan birni. (Halilu) 1 2
|