Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-17 15:49:43    
Kasar Sin da ta Brazil na kera jiragen sama cikin hadin gwiwa a kasar Sin

cri

Yau da shekaru uku da suka wuce, kamfanin kera jiragen sama na kasar Brazil da rukunin kera jiragen sama na birnin Harbin na kasar Sin sun kafa babban kamfanin kera jiragen sama mai suna Harbin Embraer cikin hadin gwiwarsu a kasar Sin don kera jigaren sama masu cin gajeren zango. Malam Roberto Rossi De Souza ya zama babban manaja na babban kamfanin nan. Da ya tabo magana a kan masana'antun kera jiragen sama da kasar Sin da ta Brazil suka kafa cikin hadin guiwarsu, sai ya bayyana cewa, wani babban dalilin da ya sa kasashen biyu suka yi haka, shi ne domin rukunin kera jiragen sama na birnin Harbin na kasar Sin yana kan matsayi mai rinjaye a fannin fasahar kera jiragen sama. Ya kara da cewa, "kamfanoninmu biyu dukanninsu sun kware sosai a wannan fanni. Sabo da rukunin kera jiragen sama na Harbin ya kafa masana'antunsa a birnin Harbin, shi ya sa mu iya yin amfani da wasu gine-ginen rukunin a birnin, wannan ya kawo mana matukar sauki. Birnin Harbin yana da dogon tarihin kera jiragen sama, rukunin kuma yana da 'yan fasaha da ma'aikata da yawa wadanda suka kware sosai wajen kera jiragen sama. Don haka mun iya samu fasahohin da muke bukata a birnin don kera jiragen sama."

Cikin yin la'akari da wadannan abubuwa ne, kasar Sin da ta Brazil suka daddale yarjejeniya a tsakaninsu yau da shekaru 6 da suka gabata, kuma a karo ne na farko kasashen biyu suka fara zuba jari cikin hadin gwiwarsu don kera jiragen sama masu cin gajeren zango. Ta hanyar kera jiragen sama, ma'aikatan kasar Sin sun kara daga matsayin fasaharsu cikin sauri sosai. Tun daga lokacin da aka fara harhada jirgin saman fasinja mai lambar ERJ145 na farko a karshen rabin shekarar 2003, har zuwa lokacin da aka samar da irin wannan jirgin sama na biyar a karshen shekarar 2004, matsakaicin yawan kwararrun ma'aikata na kasar Brazil da ake bukata wajen harhada ko wane jirgin saman ya ragu daga 54 zuwa 6. Ta haka ba ma kawai kamfanin kera jiragen sama na kasar Brazil ya kawo wa kasar Sin kyakkyawar fasahar kera jirgen sama ba, har ma ya kawo wa abokan aikinsa na kasar Sin sabuwar hanyar da ake bi wajen kula da harkokin kera jiragen sama. Malam Jiang Da, mataimakin babban manajan kamfanin Harbin Embraer ya bayyana ra'ayinsa a kan wannan cewa, "ta hanyar kera jiragen samar cikin hadin gwiwa, mun koyi abubuwa masu yawa. Alal misali, wannan aiki da ake yi a tsakanin kasa da kasa ya shafi 'yan kasuwa 670 a duniya wadanda ke samar da kayayyaki don kera jirgin sama mai lambar ERJ 145. Yawan 'yan kasuwa na Amurka da Turai da kudancin nahiyar Amurka wadanda ke da alaka da aikin harhada jirgin sama ya wuce 200. An kafa tsarin harhada jiragen sama ne bisa darikar kamfanin Brazil. Wato ana ta samar da kayayyaki daga wurare daban daban cikin lokaci don biyan bukatun da ake yi wajen harhada jiragen sama. Wanna wani bakon abu ne gare mu."

1 2