Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-14 20:03:07    
An rufe taron shekara shekara na sabuwar majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin

cri

Mijiti Aikebai'er, wani dan majalisar ya ce,"kowace kabila na da nata wakili, kome yawan mutanenta, wakilan wadannan kabilu na iya zaman daidaici da juna wajen sa hannu cikin harkokin siyasa. Sa'an nan, batutuwan da suka gabatar na da inganci, a ganina, za su iya ba da kyawawan shawarwari ga gwamnati wajen tsai da kuduri."

Babban nauyin da ke bisa wuyan majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin shi ne gabatar da ra'ayoyi da shawarwari kan manyan manufofin da ke shafar fannonin siyasa da tattalin arziki da na zaman al'umma, kuma 'yan majalisar su kan ba da shawarwarinsu ta hanyar gabatar da shirye-shirye. An ce, a gun taro a wannan karo, gaba daya aka gabatar da shirye shirye fiye da 4,700 a gun taron, wadanda ke shafar fannoni daban daban. Madam Zhang Yi, mataimakiyar shugaban kwamitin kula da shirye shiryen da aka gabatar, ta ce, abin da ke fi daukar hankulan 'yan majalisar shi ne zaman rayuwar jama'a. Ta ce,"zaman rayuwar jama'a ya kasance abin da ke jawo hankulan 'yan majalisar a kullum. Sabo da 'yan majalisar su wakilai ne na al'ummar kabilu daban daban da kuma bangarori daban daban, shi ya sa suke iya bayyana burin al'ummar da suke wakilta, misali inshorar kiwon lafiya na kauyuka da jin dadin zaman al'umma a kauyuka da ba da ilmi a kauyuka da kiyaye muhallin kauyuka da kara kudin shiga na manoma, dukansu akwai."

Bayan da aka rufe taron, za a mika shirye-shiryen da aka gabatar a hannun sassa 154 don su kula da su. Mr.Ainuvaer, wani mamba na majalisar ya ce, 'yan majalisar sun sa hannu cikin harkokin siyasa ta hanyar gabatar da shirye-shirye, don bayyana burin jama'a. Ya ce,"yanzu muna maganar batun zaman rayuwar jama'a, yaya al'umma za su iya jin dadin nasarorin da aka samo daga yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje, yaya za a iya kawo alheri ga jama'a, dukansu hakikanan abubuwa ne. Idan mun iya bayyana burin jama'a ga gwamnati yadda ya kamata a cikin wa'adin aikinsu, mu daidaita wasu hakikanan matsaloli, to, mu ba da namu taimako ke nan."(Lubabatu)


1 2 3