Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-14 20:03:07    
An rufe taron shekara shekara na sabuwar majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin

cri

Saurari

Yau a nan birnin Beijing, an rufe taron shekara shekara na farko na sabuwar majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin. A gun taron da aka shafe tsawon kwanaki 11 ana yinsa, 'yan majalisar fiye da 2000 da suka zo daga wurare daban daban na kasar Sin sun ba da shawarwarinsu kan manufofin kasar Sin da kuma batutuwan da ke daukar hankulan jama'a sosai, kuma sun yi shawarwari tare da manyan shugabannin kasar Sin kan harkokin kasar. A gun taron, 'yan majalisar sun kuma zabi sabbin shugabanninsu, ciki har da shugaban majalisar.

A gun bikin rufe taro na farko na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta 11 da aka gudanar a yau da safe, da misalin karfe 9, Mr.Jia Qinglin, wanda kwanan baya aka sake zaben shi a matsayin shugaban majalisar, ya yi jawabi a madadin sabuwar majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa, inda ya bayyana cewa, kamata ya yi sabuwar majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta saba da sabbin sauye sauyen halin da ake ciki, ta biya bukatun jama'a, ta yi amfani da fifikon da take da shi, kuma ta kara inganta ayyukan da take gudanarwa, ta yadda za ta kara ba da sabon taimako ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin da zaman al'ummarta.


1 2 3