Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-13 15:36:24    
Yawon shakatawa domin tunawa da juyin juna-hali

cri

A nan kasar Sin,ana kiran ziyarar yawon shakatawa a shiyyoyin tunawa da juyin-juya-halin da jama`ar kasar Sin suka yi a karkashin jagorancin jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin kafin kafuwar sabuwar kasar Sin wato kafin shekara ta 1949 da sunan `ziyarar yawon shakatawa mai launin ja`.Kwanakin baya ba dadewa ba,a birnin Beijing,kwamitin yin gyare-gyare da raya kasa na kasar Sin da ma`aikatar farfaganda ta kwamitin tsakiya na jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin da hukumar kula da ziyarar yawon shakatawa ta kasar Sin sun kira wani taron aiki tare don raya ziyarar yawon shakatawa mai launin ja,inda suka bayyana cewa,a cikin `yan shekaru masu zuwa,kasar Sin za ta kafa shiyyoyin yawon shakatawa 12 don tunawa da juyin-juya-halin da jama`ar kasar Sin suka yi a karkashin jagorancin jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin,yawan muhimman ni`imtattun wurare masu launin ja zai kai dari daya,ta yadda za a kafa sabon halin da ziyarar yawon shakatawa mai launin ja ke ciki a kasar Sin.

Kwamitin tsakiya na jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin da majalisar gudanarwar kasar Sin suna mai da hankali sosai kan wannan aiki.Ziyarar yawon shakatawa mai launin ja ita ce wani babban aiki mai muhimmanci a kasar Sin,ana iya cewa wannan aiki shi ne wani aiki na tattalin arziki da na al`adu da kuma na siyasa,jam`iyyar kwaminis ta kasar Sin da kasar Sin da jama`ar kasar Sin za su more daga aikin.Game da wannan,an riga an tsara hakikanan matakai don ingiza bunkasuwar ziyarar yawon shakatawa mai launin ja.


1 2