Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-12 15:20:33    
Hanyar zaman rayuwa cikin kwanciyar hankali za ta ba da taimako wajen magance ciwon sukari

cri

Manazarta na kwalejin kiwon lafiyar jama'a na jami'ar Minnesota ta kasar Amurka sun ba da rahoton cewa, sun yi wani bincike ga mata dubu 28 har na tsawon shekaru 11. Kafin aka fara binciken, dukkan wadannan mata ba su kamu da ciwon sukari da ciwace-ciwacen zuciya da hauhawar jini. Kuma lokacin da ake yin binciken, manazarta sun yi wa matan nan tambayoyi da yawa domin samun kidayar yawan kwafi da su kan sha, kuma sun yi la'akari kan abubuwan da ke haddasa ciwon sukari, kamar shekaru da haihuwa da nauyin jiki da yawan giya da a kan sha da shan taba da kuma motsa jiki da dai sauransu.

Sakamakon binciken ya bayyana cewa, idan an sha kwafi maras caffein har kofuna shida a ko wace rana, to za a rage hadarin kamuwa da ciwon sukari kashi 33 cikin dari idan an kwatanta shi da mutane marasa shan kwafi. Amma kwafi da a kan sha kullum ba shi taka muhimmiyar rawa kan rage hadarin kamuwa da ciwon sukari.

Ban da wannan kuma manazarta na jami'ar Minnesota sun yi nuni da cewa, bayan da suka yi nazari kan kayayyakin da kwafi ya kunsa, sun yi hasashen cewa, mai yiyuwa ne wasu abubuwan da ke cikin kwafi kamar magnesium sun ba da taimako kan sarrafa yawan sukari da ke cikin jini, amma ba su iya tabbatar da cewa, wani abu ne da ke cikin kwafi maras caffein yake taka muhimmiyar rawa ba, shi ya sa ana bukatar ci gaba da yin nazari a kan shi.

Amma kwararru sun bayyana cewa, shan kwafi fiye da kima zai ba da mummunar tasiri ga lafiyar jiki. Kuma game da rigakafin ciwon sukari, kiyaye motsa jiki da cin abinci yadda ya kamata dabaru ne mafi kyau.(Kande Gao)


1 2