Manazarta na kasar Finland sun gudanar da wani sabon bincike, inda suka bayyana cewa, game da mutanen da suka fi saukin kamuwa da ciwon sukari, cin abinci da kuma motsa jiki yadda ya kamata za su ba da taimako gare su wajen magance ciwon sukari.
Bisa labarin da muka samu daga kafofin watsa labarai na kasar Finland, an ce, manazarta na cibiyar nazari kan kiwon lafiyar jama'a ta kasar Finland sun gudanar da bincike kan mutane da ke fama da ciwon sukari cikin dogon lokaci. A cikin mutane 500 da aka gudanar da binciken gare su, rabi daga cikinsu sun karbi shawararin da aka ba su wajen cin abinci da motsa jiki, alal misali, ba su ci abincin da ke kunshe da kitse da yawa ba, kuma suna kara cin kayayyakin lambu, ban da wannan kuma su motsa jikinsu har tsawon mintoci 30 a ko wace rana. Sauran rabi daga cikinsu kuwa ba su yin haka. Bayan da aka gudanar da wannan bincike a gare su har shekaru 7, manazarta sun gano cewa, game da mutanen da suka karbi shawarwarin da aka ba su wajen hanyar yin zaman rayuwa, hadarin kamuwa da ciwon sukari gare su ya ragu da kashi 15 zuwa kashi 20 cikin dari idan an kwatanta shi da na sauran mutane.
To, masu sauraro, yanzu sai ku shakata kadan, daga baya kuma za mu gabatar muku da wani labari daban kan cewa, shan kwafi maras caffein zai rage hadarin kamuwa da ciwon sukari.
An yi wani babban bincike a kasar Amurka, kuma an gano cewa, shan kwafi maras caffein zai rage hadarin kamuwa da ciwon sukari.
1 2
|