Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-12 15:16:24    
Wani shahararren tauraron dan wasan sinima na kasar Sin mai suna Li Lianjie

cri

Bayan wannan, Mr Li Lianjie ya ga tilashi ne ya daina zaman rayuwarsa na yin wasan motsa jiki, kuma ya shiga rukunin daukar wasan sinima, wato ya tafi Hongkong don daukar sinima dangane da wasan Gongfu .

A cikin 'yan shekarun da suka wuce, Yawan sinimar da Li Lianjie ya dauka ya wuce goma ko fiye, sa'anan kuma Li Lianjie ya kaura zuwa kasar Amurka, ya sami sabon ci gaba wajen daukar sinima. Bi da bi ne ya dauki sinimar da ke da lakabi " Lethal Weapon 4" da sinimar "Romeo Must Die" da sinimar "Kiss of the Dragon" da sauransu.

Ko da yake Mr Li Lianjie ya sami aiki a Holliwood na kasar Amurka, anna yana ci gaba da kasancewa cikin halinsa na tsayawa tsayin daka bisa gargajiyar kasar Sin, ya bayyana cewa, a gaskiya dai mutane da yawa suna yi mini kauna sosai, kuma sun mayar da ni tamkar yadda wata alamar nuna bajinta a cikin zuciyarsu, amma duniyata tana babbar nahiyar Asiya, kodayake ka je wani gefe daban na duniya, amma sai mutanen da suke kaunar sinimar kasar Sin, ko wadanda suke kaunar sinimar nuna wasan Gongfu da Hongkong ya dauka suka fahimtarka kawai, kuma a kan hanyar da kake wucewa, ba wanda ya san ka, saboda haka, na gane sosai cewa, dole ne zan soma daga sifiri.

A shekarar 2007, Li Lianjie ya kafa wani asusu tare da kungiyar Red Cross ta kasar Sin, yana son ya yi kokarin samar da taimako ga wadanda suke fama da masifa a cikin mawuyacin hali.(Halima)


1 2