Ga ma'aikantan kwale-kwale, gasar Clipper ta kawo musu damar sanin bambancin al'adu da kuma jaruntakar kalubalantar kansu. Madam Zang Aimin, mataimakiyar magajin birnin Qingdao kuma mataimakiyar zaunannen shugaban kwamitin shirya shirin tseren kwale-kwale na gasar wasannin Olympic ta karo na 29 ta Qingdao ta gaya mana muhimmancin gasar Clipper ga garinta Qingdao. Ta ce,'Gasar Clipper ta ba da kyakkyawan taimako ga Qingdao wajen maraba da gasar wasannin Olympic ta Beijing, haka kuma ta jarraba karfinmu wajen shirya gasa, sa'an nan kuma, gasar tana taimaka mana wajen raya birnin Qingdao zuwa 'birnin wasan tseren kwale-kwale'. A matsayin birnin wasan tseren kwale-kwale, tilas ne ya sami bakuncin shirya gasannin kasa da kasa.'
Bayan da ta shiga gasar Clipper ta shekarar 2005 zuwa ta 2006 har zuwa yanzu, Qingdao ba kawai ta yi ta kyautata na'urorin da ke da nasaba da wasan tseren kwale-kwale ba a lokacin da take shirya shirin tseren kwale-kwale na gasar wasannin Olympic ta Beijing, har ma ta yada kyakkyawar siffarta da kuma gasar wasannin Olympic ta Beijing a duk duniya ta hanyar gasar Clipper da sauran manyan gasanni.
A gaskiya, wasan tseren kwale-kwale yana bukatar ma'aikata kwale-kwale da su yi kokari ba tare da kasala ba, kuma abu mafi muhimmanci shi ne a lokacin da suke tafiya a kan teku, ma'aikatan suna bukatar tinkarar mummunan yanayi da kuma al'amuran ba zata da yawa.
Mr. Robin Knox-Johnston, wanda ya fara kaddamar da gasar Clipper ya kan karfafa gwiwar saura da su yi tafiya a kan teku, in suke da dama. Saboda tafiya a kan teku ya iya canza zaman mutane.
A shekarar 2007, bayan da wannan tsoho mai shekaru 68 da haihuwa ya kammala zagaya duniya da kansa kadai ba tare da tsayawa ba a karo na 2, Mr. Robin ya gaya mana sha'awar wasan tseren kwale-kwale ta wannan tafiya. Ya ce,'Zagaya duniya da na yi a karo na 2 na da ban sha'awa ainun. Mun yi amfani da sabon kwale-kwale mai saurin tafiya. Mun taba gamuwa da babbar iska, sai ka ce kwale-kwalen yana tafiya a sararin sama, wannan na da hadari sosai.'
Ko da yake kasar Sin ta soma raya wasan tseren kwale-kwale ba da jimawa ba, kuma ma'aikatan kwale-kwale na kasar Sin suna bukatar ci gaba da ba da kokari, amma a sakamakon shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ta shekarar 2008, karin mutanen Sin za su sihga wannan wasa, za su yi gwagwarmaya da teku da kuma kalubalantar kansu.(Tasallah) 1 2
|