Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-12 15:07:24    
Gasar tseren kwale-kwale ta zagaya duniya ta Clipper ta janyo hankulan mutanen Sin

cri

In an kwatanta da wasu kasashen Turai da na Amurka, kasar Sin ta fara raya wasan tseren kwale-kwale ba da dadewa ba. Amma yanzu saboda kusantowar gasar wasannin Olympic ta Beijing ta shekarar 2008, a matsayinsa na birnin da ke ba da taimako wajen shirya shirin tseren kwale-kwale ta gasar wasannin Olumpic ta Beijing, birnin Qingdao da ke gabashin kasar Sin ya soma sa kaimi kan karin mutane da su kara fahimtarsu da kuma shiga wasan tseren kwale-kwale mai hadari kuma mai ban sha'awa.

A watan Febrairu na wannan shekara, a sansanin kwale-kwale na wasannin Olympic na kasar Sin, dubban mazaunan Qingdao sun taru domin maraba da kwale-kwale 10 masu halartar gasar tseren kwale-kwale ta zagaye duniya ta Clipper ta shekarar 2007 zuwa ta 2008, musamman ma wani babban kwale-kwale mai suna Qingdao da zai dawo garinsa.

Gasar tseren kwale-kwale ta zagaye duniya ta Clipper na matsayin daya daga gasannin tseren kwale-kwale na zagaya duniya mafi shahara a duniya, ita kuma gasar tseren kwale-kwale ta zagaya duniya daya tak a duniya da mutanen da ba 'yan wasa ba suka iya shiga. A shekarar 2006, an taba mayar da birnin Qingdao na kasar Sin a matsayin tashar yada zango a karo na farko. Amma a wannan shekara, abun da ya fi jawo hankulan mutanen Sin shi ne 'yan kasar Sin 3 sun shiga gasar a matsayin ma'aikatan kwale-kwale. Game da abubuwan da suka ji a zukatansu game da shiga gasar a karo na farko, Yan Xinmin, daya daga cikinsu ya gaya mana cewa,'Na gaskata da cewa, gasar Clipper tana da daraja sosai ga dukkan mutane. Kowa da kowa zai koyi abubuwa daban daban, zai dawo gida tare da wadannan abubuwa, zai kuma more su tare da iyalansu da abokansu, har ma za su ci gaba da nazarinsu a zukatansu a duk rayuwa. A kan hanyar zagaya duniya a wannan karo, saboda ina bukatar hada gwiwa da mutanen da suke zama a yanayin al'adu daban daban, shi ya sa na fahimci bambanci a tsakaninmu a fannin tunanin tafiya a teku, sa'an nan kuma, abu mafi muhimmanci a gare ni shi ne na san yadda zan yi hadin gwiwa da wadanda suka zama a yanayin al'adu daban daban, suna amfani da harsuna daban daban, suna kuma bin al'ada iri daban daban ta fuskar zaman rayuwa, haka kuma na san yadda zan saba da wadannan abubuwa a yanayi mai tsanani.'


1 2