A watan Agusta na shekarar 2006 da na shekarar 2007, an sami nasarar shirya gasar tseren kwale-kwale ta kasa da kasa ta 'Fatan alheri a Beijing' har sau 2 a cibiyar tseren kwale-kwale ta wasan Olympic ta Qingdao. Wadannan gasanni 2 gasanni ne da aka yi domin yin gwajin ingancin na'urorin wannan cibiya da karfinta wajen shirya shirin tseren kwale-kwale na gasar wasannin Olympic ta Beijing, shi ya sa wannan cibiya ta jawo hankali sosai a gida da kuma a ketare. Bayan da aka kaddamar da ita a matsayin kwarya-kwarya, cibiyar tseren kwale-kwale ta wasan Olympic ta Qingdao ta sami babban yabo daga hadaddiyar kungiyar wasan Olympic ta kasa da kasa da hadaddiyar kungiyar tseren kwale-kwale ta kasa da kasa da kuma 'yan wasa da malaman horas da wasanni na kasa da kasa.
Bayan gasar wasannin Olympic ta Beijing, za a raya wurin da wannan cibiya take zama zuwa wani wurin yawon shakatawa, za a kuma mayar da cibiyar a matsayin sansanin bunkasa tseren kwale-kwale na Qingdao.
Yanzu ya rage kwanaki 180 ko fiye da bude gasar wasannin Olympic ta Beijing ta shekarar 2008. Mun yi imani da cewa, za a sami nasarar shirya gasar tseren kwale-kwale ta wasannin Olympic masu sigar musamman a cikin wannan filin wasa da aka gina bisa tunanin 'shirya gasar wasannin Olympic ba tare da gurbata muhalli ba'.(Tasallah) 1 2
|