Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-11 12:23:46    
Cibiyar tseren kwale-kwale ta wasan Olympic ta birnin Qingdao

cri

Masu karatu, muna muku godiya da ci gaba da sauraren shirinmu na yau, wato yawon shakatawa a kasar Sin, wanda mu kan gabatar muku a ko wace ranar Talata.

A matsayinsa na daya daga cikin birane 6 da ke taimakawa birnin Beijing wajen shirya gasar wasannin Olympic ta shekarar 2008, birnin Qingdao zai sami bakuncin shirye-shiryen tseren kwale-kwale na gasar wasannin Olympic. Shi ya sa a karshen shekarar bara, wata cibiyar tseren kwale-kwale ta wasan Olympic ta zamani ta kafu a wannan birni. An zayyana da kuma gina wannan cibiya bisa tunanin 'shirya gasar wasannin Olympic ba tare da gurbata muhalli ba'.

Fadin cibiyar tseren kwale-kwale ta wasan Olympic ta Qingdao ya kai misalin kadada 45. Baya ga filin tseren kwale-kwale na gasar wasannin Olympic, an kuma gina sauran gine-ginen da abin ya shafa a cibiyar. A lokacin da ake yawo a wannan cibiya, an gano cewa, an gina ko wane sashen cibiyar tseren kwale-kwale ta wasan Olympic ta Qingdao bisa tunanin 'shirya gasar wasannin Olympic ba tare da gurbata muhalli ba'. A bangarori 2 na babbar madatsar hana igiyar ruwa, wadda za a mayar da ita a matsayin dandamalin 'yan kallo a lokacin gasa, an dasa jerin fitilu 2 masu amfani da karfin iska. Sa'an nan kuma, an hada manyan allunan tattara hasken rana kan rufin dakuna da filin wasan gaba daya, wannan yana da kyan gani sosai.

An yi amfani da fasahohin kiyaye muhalli a ko ina a cibiyar tseren kwale-kwale ta wasan Olympic ta Qingdao, kamar su fasahar amfani da hasken rana da fasahar amfani da bambancin zafin ruwan teku wajen samar da zafi domin dumamar daki ko kuma iskar sanyi domin sanyaya daki da fasahar ba da wutar lantarku daga karfin iska da dai sauransu.


1 2