Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-07 16:27:14    
Labari kan sake dawowar gasar wasannin Olympics a Paris

cri

Da yake kwamitin shirya wasannin Olympics na Paris ya yi shiri sosai, shi ya sa 'yan wasa fiye da 3,000 daga kasashe da yankuna 44 suka halarci wannan gagarumar gasa, har ma aka shigar da sunayen wasu nagartattun 'yan wasa daga cikinsu a cikin littafin tarihin wasannin Olympics har abadin abada. Bugu da kari, mazauna birnin Paris su ma sun nuna sha'awa sosai ga gasar wasannin Olympics, dubban 'yan kallo sun kallaci bikin bude gasar, inda cike da halin annashuwa.

Jama'a masu sauraro, ko kuna sane da cewa, a lokacin da ake gudanar da gasar wasannin Olympics ta Paris a shekarar 1924, an yanke shawara a karshe kan batun shigar mata a gun gasar wasannin Olympics. Kamar yadda kuke sanin cewa, tuni daga farkon shekarar 1900, ana ta takaddama kan batun shigar mata a gun gasar wasannin Olympics. Saboda haka, a cikin wani dogon lokaci, ra'ayin da kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa yakan dauka har kullum kan wannan batu ya yi baina-baina, sai dai har zuwa lokacin da ake gudanar da gasar wasannin Olympics a wancan gami, kwamitin ya amince da kudurin yarda da shigar mata a gun gasar wasannin Olympics a hukumance. Labuddah wannan na da muhimmancin gaske ga bunkasa sha'anin wasannin motsa jiki na mata.


1 2