Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, bayan da aka kammala gasar wasannin Olympics ta bakwai, sai aka mayar da birnin Paris na kasar Faransa a matsayin birnin da ya dauki nauyin gudanar da gasar wasannin Olympics ta takwas ta shekarar 1924, wato ke nan birnin Paris ya zama wani birni na farko da ya zama mai masaukin gasar wasannin Olympics har sau biyu a cikin tarihin wasannin Olympics. Amma duk da haka, mutane da dama sun yi shakkar cewa ko gwamnatin birnin Paris za ta iya gudanar da gasar wasannin Olympics ta shekarar 1924 da kyau sakamakon wasu rigingimu da aka yi lokacin da ake gudanar da gasar wasannin Olympics ta Paris a shekarar 1900.
Amma, abin farin ciki shi ne, yanayin wannan gami ya sha bamban da na wancan kwarai da gaske. Bayan da kwamitin wasannin Olympics na kasa da kasa ya shelanta cewa birnin Paris ya samu iznin shirya gasar wasannin Olympics, sai 'yan kasar Faransa suka nuna zafin nama sosai, kuma mutane masu tarin yawa daga cikinsu sun gabatar da shawarwarinsu masu amfani ga kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na Paris kan yadda za a gudanar da gasar lami-lafiya.
Domin bada tabbaci ga gudanar da gasar din kamar yadda ya kamata, kwamitin shirya wasannin Olympics na Paris ya kaddamar da ka'ida da kuma ajandar dukkan gasanni ; A lokaci guda, ya nemi hadaddun kungiyoyin wasannin motsa jiki daban-daban na duniya da su fito da dokoki kan gasanni da kuma kula da ayyukan alkalai da na sa ido kan gasanni.
1 2
|