Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-05 20:33:24    
Asibitin moriyar jama'a ya kawo alheri sosai ga fararen hula da ke da zaman rayuwa mafi kankanta

cri

Lokacin da aka ambaci amfanin manufofin moriyar jama'a wajen tallafa wa fararen hula masu fama da talauci wajen ganin likita, shugaban asibitin Red Cross na birnin Nanjing Li Yuanhuai ya bayyana cewa, "lalle manufofin sun warware wasu matsalolin da fararen hula masu fama da talauci ke fuskanta. Ganin likita yana da wuya da kuma tsada wata muhimmiyar matsala ce ga zaman al'umma. Game da mutane masu fama da talauci, kudaden da aka ba su suna iya warware matsalar abinci kawai, ba su iya warware matsalar samun jiyya ba. Shi ya sa aiwatar da manufofin ba da gatanci na musamman yana iya warware matsalar samun jiyya da fararen hula dubu 130 masu fama da talauci na birnin Nanjing ke fuskanta."

Asibitin moriyar jama'a ya yi kwarjini sosai a cikin zukatan mazaunan birnin Nanjing bisa farashi mai araha da kuma ayyukan ba da hidima mai inganci. Haka kuma irin wannan amincewa da jama'a ke nunawa ita ma ta inganta ci gaban asibitin.

To, jama'a masu sauraro, shirinmu na yau na kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin ke nan. Muna fatan kun ji dadinsu, da haka Kande ce ke shirya muku wannan shiri kuma ke cewa a kasance lafiya.(Kande Gao)


1 2