Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-05 20:33:24    
Asibitin moriyar jama'a ya kawo alheri sosai ga fararen hula da ke da zaman rayuwa mafi kankanta

cri

Assalamu alaikum, jama'a masu sauraro, barkanku da war haka. Barkanmu da sake saduwa a wannan fili na "kimiyya da ilmi da kuma kiwon lafiya na kasar Sin". Ni ce Kande ke gabatar muku da wannan shiri. A cikin shirinmu na yau, za mu leka asibitin Red Cross na birnin Nanjing na lardin Jiangsu da ke gabashin kasar Sin. Asibitin ba wani asibitin yau da kullum ba ne, yana shahara kwarai da gaske sabo da karbar kudaden ganin likita kadan, da samar da kyawawan ayyukan ba da hidima don fararen hula masu fama da talauci, shi ya sa fararen hula su kan kira shi "asibitin moriyar jama'a". Haka kuma wannan gwaji ne da birnin Nanjing ya yi wajen yin gyare-gyaren tsarin jiyya domin kowa da kowa yana iya samun ayyukan ba da hidima a fannin jiyya. To, yanzu ga cikakken bayani.

An kafa asibitin Red Cross na birnin Nanjing a shekara ta 2002. Madam Luo Yiying da ke fama da cutar sankara tana kwance a cikin asibitin wajen samun jiyya. Diyarta Zhou Sibao ta gaya mana cewa, "muhallin wannan asibiti yana da kyau, muna iya kallon talibijin. Haka kuma asibitin ya samar da ayyukan ba da hidima masu inganci, nus-nus da likitoci suna da kirki kwarai da gaske."

Madam Luo mai shekaru 73 da haihuwa tana da yara biyar, amma dukkansu ba su samu guraban aikin yi yanzu. Yau da shekaru da dama da suka gabata, an tabbatar da cewa, Madam Luo ta kamu da sankarar huhu, sabo da haka an kara nauyin da ke bisa wuyan gidanta a fannin tattalin arziki. Diyarta Zhou Sibao ta nuna damuwa sosai a kan batun, amma abin sa'a shi ne, asibitin moriyar jama'a ya warware matsalar, kuma ta bayyana cewa, "Ba mu da aikin yi, amma mahaifiyata ta kamu da wannan cuta. In mun je babban asibiti, dole ne za mu kashe kudade dubu gomai, ba mu iya daure wannan nauyi ba. Yanzu gwamnatin Nanjing ta kafa asibitin moriyar jama'a, lalle yana da matukar kyau. An rage dimbin kudaden jiyya da muka kashe."

Asibitin moriyar jama'a ya samar da manufofin rage yawan kudade da na ba da gatanci iri 13 ga mutanen da ke kamuwa da cututtuka wadanda hukumar kula da harkokin jama'a ta tabbatar da cewa, suna fama da talauci sosai. Muddin mutanen da ke kamuwa da cututtuka sun je asibitin tare da takardar ba da tabbaci ga jama'a da ke da zaman rayuwa mafi kankanta, to za su iya samu gatanci. Ba kawai an soke dukkan kudaden ragista da ganin likita da kuma kulawa ba, har ma an rage rabin kudaden gadaje da yin tiyata da kuma bincike.

1 2