Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-05 09:28:30    
Direbobin Taxi na birnin Beijing suna kokarin kyautata ingancinsu domin tarye gasar wasannin Olympic ta shekarar 2008

cri

A gun gasar wasannin Olympic ta birnin Beijing, masu yawon shakatawa da 'yan kallo da yawan gaske za su zo birnin daga kasashen waje, shi ya sa Wang Jiansheng ya yi kokarin koyon turanci, ya ce: "Yanzu ina yin kokarin kago muhallin koyon turanci, a kullum na yi hira da fasinja da turanci, a kwana a tashi, matsayin turancina ya dada daguwa."

Wata rana, wata tsohuwa daga kasar waje ta shiga taxi na Wang Jiangsheng a filin jirgin sama na kasa da kasa na birnin Beijing domin zuwa Jianguo otel, amma ba ta iya sinanci ba, sai Wang Jiansheng ya yi magana da ita da turanci, ta ji mamaki, kuma ta ji farin ciki. A wannan rana da dare, ta buga waya ga Wang Jiansheng inda ta roke shi da ya je filin jirgin sama domin daukar abokanta biyu. Game da wannan, Wang Jiansheng ya ce:  "Na samar da hidima mai kyau ga baki daga kasashen waje, na nuna musu ingancin direbobin kasar Sin, ban da wannan kuma, kudin hayar mota da na samu shi ma ya karu."

A halin da ake ciki yanzu, bakin da suka zo birnin Beijing daga kasashen waje sun kara karuwa, wannan ya kawo wa Wang Jiansheng iznin aiki da yawa, Wang Jiansheng shi ma ya dauka cewa, turanci yana da muhimmanci sosai ga aikinsa, ya ce:  "Yawancin abokan kasashen waje suna jiran gasar wasannin Olympic ta birnin Beijing tare da mu, shi ya sa direbobin taxi na birnin za su kara samun iznin ba da hidima ga bakin kasashen waje. Ina ganin cewa, kamata ya yi direbobin taxi su kara yin kokarin koyon turanci." (Jamila Zhou)


1 2