Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-05 09:28:30    
Direbobin Taxi na birnin Beijing suna kokarin kyautata ingancinsu domin tarye gasar wasannin Olympic ta shekarar 2008

cri

Yayin da gasar wasannin Olympic ta birnin Beijing ke kara kusantowa, sana'o'i daban daban na birnin suna sanya namijin kokari, sana'ar hayar mota wato taxi ita ma ta yi kokari. Don daukan baki na gida kasar Sin da na kasashen waje a gun gasar wasannin Olympic, direbobin taxi na birnin Beijing suna yin matukar kokari domin kyautata ingancinsu da kuma daga matsayinsu na ba da hidima. A cikin shirinmu na yau, bari mu kawo muku bayani kan wannan.

Kamar yadda kuka sani, sana'ar taxi tana da muhimmanci sosai, Da zarar wani bako ya sauka a wani birni, kila ne mutum na farko da zai gamu da shi direban taxi ne, shi ya sa ana iya cewa, ingancin direban taxi ya nuna mana matsayin bunkasuwar wayin kai na wani birni. Yanzu, da gasar wasannin Olympic ta birnin Beijing tana kara kusantowa, direbobin birnin suna daukan hakikanan matakai don ba da gudumuwarsu. Wang Jiansheng, direban kamfanin taxi na arewa na birnin Beijing shi ne daya daga cikinsu.

Wakilinmu ya ziyarci Wang Jiansheng ne a cikin motarsa, a kan motarsa, ana iya ganin wata alama mai ma'anar 'direbobi dari daya mafiya nagarta'. Wang Jiansheng ya gaya mana cewa, kafin wannan, ya taba yin aiki a kamfanoni daban daban, alal misali, kamfanin gwamnati da kamfanin kauye da kuma kamfanin jarin waje, yanzu yana aiki a kamfanin taxi na arewa na birnin Beijing. Wang Jiansheng ya ce:  "Abu mafi muhimmanci shi ne ina kaunar wannan aiki, wato ina kaunar tuka taxi." Kodayake Wang Jiansheng ya sha aiki kowace rana, amma yana jin dadi, dalilin da ya sa haka shi ne domin yana ganin cewa, aikinsa yana da amfani wajen bauta wa gasar wasannin Olympic. Ya ce:  "Na ji dadin aikina sosai da sosai, ina ganin cewa, wannan aiki shi ne jami'a ta musmaman, kowace rana na koyi ilmomi daban daban daga fasinjoji daban daban."

Tun daga shekarar 2005, birnin Beijing ya dauki matakai daban daban don kara daga matsayin hidima na taxi, gwamnatin birnin Beijing ita ma ta bukaci dukkan direbobin taxi na birnin da su daga matsayinsu domin gabatar da fasahar hidima mafi kyau da matsayin hidima mafi kyau da kuma sakamakon hidima mafi kyau ga gasar wasannin Olympic.

1 2