Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-03 16:18:36    
Ana kyautata zaman manoman kauyen 'Matouchuan' a kasar Sin ta hanyar ba da taimakon kudi

cri

Manomi Wang ya kan kashe kudi mai yawa domin yaransa uku da ke karatu a makarantar sakandare ta gunduma Longxi. Ya ce, yawan kudin da ya samu daga wajen wurinsa na sarrafa alkama da abincin dabbobi da tsire-tsiren hada magunguna ya wuce kudin Sin Yuan dubu 20 a shekarar bara, don haka zaman rayuwar iyalinsa ya kyautatu sosai idan an kwatanta shi da na shekarun baya.

Wani manomi daban mai suna He Junming wanda ke da shekaru 67 da haihuwa a bana shi ma ya taba samun rancen kudin Sin Yuan dubu 3 daga asusun kauyen Matouchuan musamman domin kiwon dabbobin gida. Yanzu yana samun kudin shiga musamman daga wajen noman masara da aikin kiwon dabbobi. Manomi He Junming ya bayyana cewa, "gaskiya ne, asusun kauyenmu yana da kyau, muna cin gajiyarsa kwarai."

An ruwaito cewa, ya zuwa karshen shekarar bara, manoma masu fama da talauci sama da 500 na kauyukan biyar na gundumar Longxi ta lardin Gansu da ke a arewa maso yammacin kasar Sin sun kara kyautata zaman rayuwarsu, ta hanyar yin aikin kiwon dabbobi da na sarrafa amfanin gona da sufuri da sauran sana'o'i, bisa rancen kudin da suka samu daga wajen asusun kauyukansu. (Halilu)


1 2