Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-03-03 16:18:36    
Ana kyautata zaman manoman kauyen 'Matouchuan' a kasar Sin ta hanyar ba da taimakon kudi

cri

Kauye mai suna Matouchuan yana a gundumar Longxi ta jihar Gansu da ke a arewa maso yammacin kasar Sin, a da wannan kauye wani kauye ne mai talauci kwarai. Amma a cikin shekarun nan da suka wuce, bisa taimakon kudin da ake samarwa cikin hadin gwiwa, zaman rayuwar manoman kauyen kullum sai kara kyautatuwa yake yi, kauyensu ma ya sami manyan sauye-sauye.

A shekarar 2006, gwamnatin kasar Sin ta zabi jihar Gansu da ta Xinjiang ta kabilar Uygur mai ikon aiwatar da harkokin kanta da sauran jihohi 12 wadanda ke koma baya a fannin tattalin arziki, don gwajin ba da taimakon kudi cikin hadin gwiwa a kauyuka. Wato ta ware kudinta mai yawa don kafa asusun tallafa wa matalauta a wasu kauyuka da ke fama da talauci na wadannan jihohi. Haka kuma iyalan manoma na kauyukan ma su iya ba da kudinsu ga asusun ta yadda manoman za su ci bashi daga asusun don bunkasa aikin noma da sauran sana'o'i.

Malam Zhang Jing, wani jami'in hukumar kula da harkokin tallafa wa matalauta ta gundumar Longxi ya bayyana cewa, a farkon shekarar 2006, an kafa irin wannan asusun a kauyen Matouchuan da sauran kauyuka uku na gundumar, don taimaka wa manoma wajen bunkasa sana'o'insu. Ya kara da cewa, "makasudin kafa asusun a kauyukanmu shi ne, musamman domin kawar da karancin kudin da manoma ke yi wajen bunkasa sana'o'insu, ta yadda manoma masu fama da talauci za su kara samun karfinsu wajen bunkasa sana'o'insu cikin gashin kai. Haka kuma mun yi la'akari sosai da sahihanci da dimokuradiyyar da manoma ke nunawa ga asusun."

A kauyen Matouchuan, hukumar ta samar da kudin Sin Yuan dubu 150, manoma kuma sun ba da kudin Sin Yuan 200 zuwa 400 don kafa asusun tallafa wa matalau. Manoman sun zabi kwamitin kula da asusun ta hanyar dimokuradiyya, don sanya wa juna ido da gudanar da asusunsu da kyau. A shekarar 2006, manomi Wang Youyu ya shiga cikin asusun kauyen nan. Da matarsa ta tabo magana a kan wannan, sai ta ce, "a ganina, yawan ruwan rancen kudin da muke biya wa asusun kauyanmu ya yi kasa da na banki, haka kuma muna samun irin wannan rancen kudi cikin sauki."

Manomi Wang Youyu shi ma ya bayyana cewa, a farkon shekarar bara, ya sami rancen kudin Sin Yuan 3,000 daga asusun kauyensu, ya kuma kashe kudin Sin Yuan 7,000 bisa aljihunsa, ya sayi wata kyakkyawar na'urar gyara alkama don kafa wurin sarrafa alkama da abincin dabbobi. Yanzu yawan kudin shiga da yake samu ya karu sosai. Ya kara da cewa, "yanzu, muna samun isasshen kudi wajen sayan kayayyakin abinci da sabbin tufafi domin yara."

1 2