Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-29 15:29:48    
Tarihin Ban Ki-Moon

cri

A ran 9 ga watan Oktoba na shekarar 2006, gaba daya ne kasashe 15 da ke cikin kwamitin sulhu na MDD suka amince da gabatar da Ban Ki-moon a matsayin babban sakataren MDD, kuma a ran 13 ga watan, an gudanar da cikakken babban taron MDD, inda wakilan kasashe mambobi 192 mahalarta taron suka zartas da kudurin nada ministan harkokin waje da kasuwanci na Koriya ta kudu, Ban Ki-Moon a matsayin sabon babban sakataren MDD.

A ran 14 ga watan Disamba na shekarar, Ban Ki-Moon ya yi rantsuwar kama mukamin babban sakataren MDD, wato ke nan, ya kasance babban sakatare na 8 a tarihin MDD, kuma wa'adin aikinsa zai kammala a ran 31 ga watan Disamba na shekarar 2011.

Bayan aiki, Ban Ki-Moon yana kuma da iyalan da ke zaman farin ciki. Matarsa abokiyar karatunsa ce a makarantar sakandare, kuma suna da 'ya'ya uku. A ganin matarsa da kuma 'ya'yansu, Ban Ki-Moon miji ne mai kyau, haka kuma mahaifi ne mai kyau.(Lubabatu)


1 2