A wannan mako, za mu amsa tambayar malam Babangida Sa'id, mai sauraronmu da ya zo daga jihar Bauchi, tarayyar Nijeriya. A cikin wasikar da malamin ya turo mana, ya ce, don Allah, a ba ni tarihin Ban Ki-moon, babban magatakarda a MDD. To, masu sauraro, yanzu sai a gyara zama, a sha wani bayani game da tarihin babban sakatare mai ci yanzu na MDD, Mr.Ban Ki-moon.
An haifi Ban Ki-moon ne a watan Yuni na shekarar 1944 a wani gidan manomi da ke kudancin kasar Koriya ta kudu. Tun lokacin da yake karami, burinsa shi ne zama wani jami'in diplomasiyya, sabo da haka, ya yi matukar kokarin koyon Turanci. Har ma a lokacin da yake makarantar sakandare, ya taba zuwa kasar Amurka karatu, a matsayinsa na daya daga cikin dalibai hudu da suka sami kudin sukolashif na gwamnatin Amurka a duk fadin Koriya ta kudu. Daga baya, a shekarar 1970, Mr.Ban Ki-moon ya gama karanta ilmin diplomasiyya tare da samun maki mai kyau daga jami'ar Seoul ta Koriya ta kudu.
Bayan da ya gama karatu a jami'a, Ban Ki-moon ya ci jarrabawar zama babban jami'in ma'aikatar harkokin waje ta Koriya ta kudu, kuma daga nan ne, ya fara taka rawa a fagen diplomasiyya. Bi da bi ne ya kama mukaman mataimakin karamin jakada a ofishin jakadancin kasar Koriya ta kudu da ke kasar Indonesia da karamin jakadan Koriya ta kudu a kasar Amurka da shugaban sashen kula da manufofi na ma'aikatar harkokin waje ta Koriya ta kudu da mataimakin ministan harkokin waje na farko na Koriya ta kudu da jakadan Koriya ta kudu a kasar Austria da mataimakin ministan kula da harkokin diplomasiyya da kasuwanci na Koriya ta kudu da jakadan Koriya ta kudu a MDD da ministan kula da harkokin waje da kasuwanci na Koriya ta kudu.
Bayan ayyukan diplomasiyya, Mr.Ban Ki-moon ya kuma taba rike muhimman mukamai a cikin gwamnatin Koriya ta kudu.
A matsayinsa na wani jami'in diplomasiyya, Mr.Ban Ki-Moon ya kasance mutum mai fara'a da walwala, kuma ya iya saurin tunani da kuma mu'amala da jama'a sosai. Sabo da kullum yana sakin fuska a fagen diplomasiyya, shi ya sa kafofin yada labarai na kiransa "jami'in diplomasiyya mai fara'a", a yayin da takwarorinsa suke bayyana shi a matsayin "mutum mai kwazo kuma mai iya magana da kuma mai kyakkyawan tunani,"
Kasancewarsa wani babban jami'in diplomasiyya, daidaita batun nukiliyar zirin Koriya wata babbar matsala ce a gabansa bayan da ya kama mukamin ministan harkokin waje da kasuwanci na Koriya ta kudu a watan Janairu na shekarar 2004. Sabo da haka, ya yi kokarin gudanar da aikin diplomasiyya a tsakanin kasashen da abin ya shafa, har ma ya zamanto wani muhimmin mutum daga bangaren Koriya ta kudu a gun shawarwarin da aka yi tsakanin bangarori shida a kan batun nukiliyar zirin Koriya. Bisa kokarin da ya yi, an kuma amince da rawar musamman da Koriya ta kudu ta taka a wajen daidaita matsalar, kuma an daga matsayinta a duniya.
1 2
|