Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-27 15:09:51    
Kasashen Sin da Amurka sun sami ra'ayi iri daya wajen cigaba da kara yin shawarwari da hadin gwiwa da aminci

cri


Wen Jiabao da Rice

Mr. Yang Jiechi ya jaddada cewa, batun Taiwan ya shafi ikon mulki da cikakken yankin kasar Sin. Kasar Sin ta yabawa kasar Amurka ta nuna adawa da "kada kuri'ar raba gardama don shigar Taiwan cikin MDD" ya ce, "game da batun Taiwan, kullum muna tsayawa tsayin daka kan manufar "aiwatar da tsari iri 2 a cikin kasa daya, da sanu hadin kan kasa ta hanyar zaman lafiya", dukkan jam'iyyun Taiwan wadanda suka aminci da ka'idar kasar Sin daya, za mu son yin shawarwari tare da su kan ko wane iri batutuwa."
Game da batun nukiliyar zirin Korea, bangarorin biyu sun yabawa yunkurin shawarwarin bangarorin shida. Mr. Yang Jiechi ya jadadda cewa, kasar Sin tana fatan bangarori daban dabam su girmama nasarorin da aka samu, da kuma kara yin shawarwari domin sa kaimi ga wannan yunkuri. Ya ce, yanzu bangarori daban dabam suna rike tumtuba da juna, kasar Sin tana yin musanyar ra'ayoyi tare da kasar Korea ta arewa domin shimfida ayyuka na zagaye na biyu, kasar Sin tana fatan za a shimfida ayyuka na zagaye na biyu a dukkan fannoni. Kuma za ta cigaba da yin kokari domin sa kaimi ga shawarwarin bangarori shida.
Madam Rice ta yi alkawarin cewa, "mun riga mun yi tattaunawa kan matsalar nukiliya da sakamakon da aka samu wajen lalata nukiliya a kasar Korea ta arewa, muna fatan kasar Korea ta arewa za ta cika alkawarinta."
Ban da haka kuma, Madam Rice ta yabawa kokarin da kasar Sin ta yi wajen warware matsalar Darfur. Yayin da ta gana da firaminista Wen Jiabao, ta nuna cewa, hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Amurka da Sin zai ba da taimakawa wajen warware matsaloli masu wuya da kasashen duniya ke fuskanci.
A ran 26 ga wata da dare, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya gana da Madam Rice, ya nuna cewa, yana fatan kasashen Sin da Amurka za su cigaba da manufar yin hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, ta haka domin sa kaimi ga bunkasuwar huldar da ke tsakaninsu yadda ya kamata.


1 2