Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-27 15:09:51    
Kasashen Sin da Amurka sun sami ra'ayi iri daya wajen cigaba da kara yin shawarwari da hadin gwiwa da aminci

cri

Hu Jintao da Rice

A ran 27 ga wata, Madam Condoleezza Rice sakatariyar harkokin waje ta kasar Amurka ta tashi daga nan birnin Beijing ta gama ziyararta na karo na hudu cikin wa'adinta a kasar Sin. Madam Rice ta yi kwana daya kawai a kasar Sin, amma bi da bi ne ta gana da shugaba Hu Jintao, da firaminista Wen Jiabao, da Memban majalisar gudanarwa Tan Jiaxuan na kasar Sin, wannan ya nuna kyakkyawan yanayin da ke tsakanin kasashen biyu da hankali sosai da kasar Sin ta mayar kan ziyarar Rice. Abin da ya jawo hankulan kasa da kasa shi ne, kasashen Sin da Amurka sun sami ra'ayi iri daya wajen cigaba da kara yin shawarwari da hadin gwiwa da aminci.

 
Ran 26 ga wata da safe a karfe 11 da rabi, Madam Rice ta yi shawarwari tare da Mr. Yang Jiechi ministan harkokin waje na kasar Sin. Bayan wannan shawarwari, Mr. Yang Jiechi ya ce, "Muna yabawa cigaban da aka samu kan huldar da ke tsakanin kasashen biyu, muna fatan za a cigaba da aiwatar da manyan ra'ayoyin da shugabannin kasashen biyu suka samu, da kuma karfafa yin hadin gwiwa kan fannonin tattalin arziki da ciniki, da yaki da ta'addanci, da makamashi, da kiyaye muhalli, bisa ka'idar girmamawa juna, da moriyar juna cikin adalci, da rashin tsoma baki kan harkokin gida."


A cikin shekarun baya, manyan jami'an kasashen biyu suna tumtubar juna, kuma kasashen biyu sun hada kansu da yin musanya kan batutuwan yankuna da kasashen duniya, wannan ya zama wata sabuwar nasara yayin da ake bunkasa huldar da ke tsakaninsu.

 
Game da batun Taiwan, sanarwar tarayya guda 3 da kasashen Sin da Amurka suka daddale su ne babban tushen bunkasuwar huldar da ke tsakaninsu lami lafiya. A cikin sama da shekaru 20 da suak wuce, kasar Amurka ta yi alkawarin tsayawa tsayin daka kan manufar kasar Sin daya tak a duniya, wannan ya bayar da moriya ga kasar Amurka sosai. Madam Rice ta ce, "Kasar Amurka za ta cigaba da aiwatar da ka'idar kasar Sin daya tak a duniya, kuma muna adawa da wasu canje-canje da suka faru a Taiwan, muna fatan za a iya warware wadannan batutuwa ta hanyar zaman lafiya. Na sake jaddada kasar Amurka tana adawa da Taiwan ta 'kada kuri'ar raba gardama don shiga cikin MDD'."


1 2