Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-27 12:45:06    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(21/02-27/02)

cri

Ran 21 ga wata, hadaddiyar kungiyar wasan kwallon badminton ta kasa da kasa ta kaddamar da sabon jerin 'yan wasa na duniya. Ba a canza dukan 'yan wasan da suka zama na farko a cikin shirye-shirye 5 bisa wannan sabon jeri ba, dukansu 'yan wasan kasar Sin ne. 'Yan wasan Sin mata sun sami rinjaye sosai a cikin gasa ta tsakanin mace da mace da kuma gasa ta tsakanin mata biyu biyu.

Ran 21 ga wata, a birnin Lausanne, Switzerland, kwamitin wasan Olympic na kasa da kasa ya sanar da cewa, za a yi gasar wasannin Olympic ta matasa a karo na farko a kasar Singapore a shekarar 2010. Ko da yake birnin Moscow na kasar Rasha ita ma ta nemi samun bakuncin wannan muhimmiyar gasa ta matasa, amma a karshe dai, kasar Singapore ta sami amincewa daga mambobin kwamitin wasan Olympic na duniya.

A gun cikakken taro da kwamitin wasan Olympic na duniya ya shirya a shekarar bara, dukan masu halartar taron sun yarda da shirya gasar wasannin Olympic ta matasa. 'Yan wasa masu shiga gasar shekarunsu ya tashi tsakanin 14 zuwa 18 da haihuwa. Za a yi irin wannan gasa ta lokacin zafi a watan Agusta na shekarar 2010, za a kuma yi irin wannan gasa ta lokacin hunturu a shekarar 2012.(Tasallah)


1 2