Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-27 12:45:06    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(21/02-27/02)

cri

Dangane da aikace-aikacen da wasu kungiyoyi masu zaman kansu suka yi a kwanan baya, wato sun yunkura domin sanya dalilin siyasa kan gasar wasannin Olympic ta Beijing, sun kuma matsa wa kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa lamba bisa wannan, a ran 22 ga wata, a lokacin da yake zantawa da kafofin yada labaru na kasar Amurka, shugaba Jacque Rogge na kwamitin wasannin Olympic na duniya ya bayyana cewa, gasar wasannin Olympic ba ta iya warware dukan matsalolin da kasashen duniya ke fuskanta ba.

Ya kuma kara da cewa, kwamitin wasan Olympic na duniya wata kungiyar wasa ce ba ta siyasa ba, bai iya warware dukan matsalolin da kasashen duniya ke fuskanta ba. Wasu kungiyoyi masu zaman kansu sun nemi yin amfani da tasirin da gasar wasannin Olympic ta Beijing ta bayar domin gudanar da batutuwansu, ba za a iya hana irin wannan lamari ba. Ko da yake gasar wasannin Olympic wani irin karfi ne mai yakini, amma ta gaza wajen yin abubuwa fiye da karfinta.

Sa'an nan kuma, ya jaddada cewa, masu shirya gasannin wasannin Olympic na da sun sha gamuwa da dimbin suka. Sabani da zargi wani bangare ne na gasar wasannin Olympic.

A ran 24 ga wata, a birnin Guangzhou da ke kusancin kasar Sin, an bude gasar fid da gwani ta wasan kwallon tebur a tsakanin kungiya-kungiya ta duniya a karo na 49. A cikin gasa ta farko, kungiyoyin kasar Sin maza da mata sun lashe abokan takararsu duka.


1 2