Kazalika kuma, bayan da aka kammala shimfida wurin gasa a cikinsa, nan gaba ba da jimawa ba za a yi amfani da dakin aikin horaswa na farko da aka ajiye injunan sanyaya daki a ciki a tarihin wasa da dawaki na gasar wasannin Olympic. Za a yi shirin wasa da dawaki na gasar wasannin Olympic ta Beijing a ran 11 zuwa ran 13 ga watan Agusta na shekarar da muke ciki, lokacin can lokaci ne da Hong Kong ta shiga lokacin zafi. An shimfida wurin gasa mai tsawon mita 70, kuma mai fadin mita 35 a wannan dakin aikin horaswa mai amfani da injunan sanyaya daki a ciki. Ta haka, dawaki masu halartar gasar za su ci gaba da aikin horaswa a lokacin zafi.
Baya ga yin amfani da na'urorinta da kuma kashe kudin Hong Kong fiye da miliyan 800 wajen yin kwaskwarima da fadada filayen wasa, hadaddiyar kungiyar tseren dawaki ta Hong Kong za ta kuma ba da goyon baya ta fuskar guzuri wajen shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing da ta nakasassu a fannoni daban daban a matsayin wata kwararriya, kamar su samar da motocin yin jigilar dawaki da asibitocin dawaki da tashoshin bincike a filin wasa da dawaki a Beijing.
1 2 3
|