Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-26 08:44:55    
Bukukuwan wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin masu ban sha'awa a bikin bazara

cri

Za a yi bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin a wurin yawon shakatawa na Ditan tun daga ran 6 zuwa ran 13 ga wata. Za a nuna sigar musamman ta tsarin gine-gine na titunan Beijing, wato katangu da fale-falen burki da jinka masu launin toka-toka, ta haka mutane za su iya yawo a cikin lungunan gargajiya na Beijing a zamanin da. A lokacin da ake yin wannan biki, za a nuna wasannin kwaikwayo game da aikin sadaukarwa a ko wace rana da safe a nan. Ta haka, masu yawon shakatawa za su iya ganin yadda sarakunan zamanin daular Qing na kasar Sin suka yi bikin sadaukarwa domin neman tabbatar da kwanciyar hankali a kasar Sin da kuma yin girbi mai armashi da kuma samun yanayi mai kyau yau da shekaru fiye da 100. Ban da wannan kuma, sun iya kara saninsu kan al'adun gargajiya da yawa da mazauna Beijing suka bi a zamanin da.

Shekarar bana, shekara ce ta bera, wato bera ta zama alamarta a kasar Sin. shi ya sa hukumar shirya bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin a wurin yawon shakatawa na Ditan ta kera abubuwan nuna fatan alheri masu nuna sigar musamman ta shekarar Bera, wato kyawawan mutum-mutumi na beraye 2 da aka yi da tabo, za a sayar da su kadan. Wadannan kyawawan beraye 2 masu launin ja da na rawaye sun sa hannunsu a baya, sun daga kansu. A lokacin bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya, za su yi maraba da masu yawon shakatawa daga wurare daban daban cikin murmushi. Kazalika kuma, saboda za a yi gasar wasannin Olympic ta Beijing a wannan shekara, shi ya sa za a bayyana alamun wasannin Olympic a gun bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin a wurin yawon shakatawa na Ditan. Zhang Jinsong ya yi mana karin bayani cewa,

'Za a yi gasar wasannin Olympic a nan Beijing a wannan shekara. Unguwar Dongcheng unguwa ce daya kacal daga cikin unguwanni 4 na yankin tsakiya na Beijing da za a yi shirye-shiryen gasars wasannin Olympic, wato shirin wasan dambe. Za mu fito da dandamalin kara fahimta kan wasan dambe, ta haka mutane za su fahimci yanayin gasanni kafin gasar wasannin Olympic ta Beijing. Masu yawon shakatawa za su iya samun aikin horaswa daga 'yan wasan dambe, za su kuma iya yin takara da su.'

Titin sayar da kayayyaki masu nuna sigogin musamman da za a bude a gun bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin a wurin yawon shakatawa na Ditan shi ma zai janyo hankulan mutane sosai, inda za a sayar da kayayyakin fasaha na gargajiya na kasar Sin da aka yi da hannu. Wasu kayayyakin wasa na yara masu dogon tarihi za su ba yara na yanzu mamaki kwarai, domin ba su ga taba ganin irinsu a da ba, sai a gun bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin. A lokacin da suke halartar bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin, masu yawon shakatawa za su sayi zane-zanen takarda da aka yanke da almakashi da takardun fatan alheri da aka manna su a kofa, ta haka za su koma gida tare da fatan alheri.

A gabashin birnin Beijing, a kan yi bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin a gidan ibada na Dongyuemiao, shi ne daya daga cikin bukukuwan wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin masu dogon tarihi a Beijing. A bikin bazara na wannan shekara, za a yi bikin nune-nunen kayayyaki game da bera a gidan ibadar. Za a yi bayani kan al'adu dangane da alamar shekarar haihuwa ta bera ta hanyar nuna abubuwan al'umma kusan dari 1 tare kuma da hotuna da bayanai.


1 2 3