Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-26 08:44:55    
Bukukuwan wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin masu ban sha'awa a bikin bazara

cri

A lokacin bikin bazara, fararen hula na kasar Sin sun fi sha'awar halartar bukukuwan wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin. Kullum a kan shirya irin wadannan bukukuwa a gidajen ibada ko kuma wuraren yawon shakatawa, inda ake iya yin harkokin nishadi da yawon shakatawa da kuma saye-saye. Sa'an nan kuma, bukukuwan wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin sun taka muhimmiyar rawa wajen nuna al'adun gargajiya na kasar Sin. A matsayinsa na wani birni na al'ada mai dogon tarihi, birnin Beijing ya fi shahara bisa wadannan bukukuwan wasannin kwaikwayo na gargajiya. A cikin shirinmu na yau, za mu zagaye a wannan birni domin halartar bukukuwan wasannin kwaikwayo na gargajiya tare, mun yi imani da cewa, tabbas ne za ku kara saninku.

Bukukuwan wasannin kwaikwayo na gargajiya na Beijing sun yi kama da lunguna da kuma gidaje masu tsakar gida irin na gargajiya a Beijing, dukkansu alamu ne na wannan birni ta fuskar tarihi. An ce, an fara shirya bukukuwan wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin a nan Beijing yau da shekaru dubu 1 ko fiye. Asalinsu harkokin sadaukarwa ne da aka yi domin addini, amma a lokacin da ake yin harkokin sadaukarwa, an kuma gudanar da wasu harkokin kasuwanci. Sannu a hankali bukukuwan wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin na yanzu sun zama wani wurin da mutane suka sake saduwa da juna da kuma yin saye-saye a lokacin bikin bazara.

Bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin da aka yi a wurin yawon shakatawa na Ditan na daya daga cikin irin wadannan bukukuwa a nan Beijing. A kan yi harkokin nishadi na gargajiya da dimbin fararen hula suke nuna sha'awa a kai. An gina wurin yawon shakatawa na Ditan a shekarar 1530, fadinsa ya wuce kadada 40, shi ne wurin da sarakunan gargajiya su kan yi bikin sadaukarwa domin nuna girmamawa ga kasa. Zhang Jinsong, wani jami'in kwamitin shirya bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin a wurin yawon shakatawa na Ditan ya yi mana karin bayani cewe, a shekarun baya, yawan masu yawon shakatawa da suka halarci bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin a wurin yawon shakatawa na Ditan ya kai misalin miliya 1 a ko wace shekara. Karin masu yawon shakatawa da suka zo daga sauran wuraren kasar Sin har ma daga ketare sun mai da hankulansu kan yanayin musamman da aka samu a gun bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin a wurin yawon shakatawa na Ditan. Ya gaya mana cewa,

'Ma iya cewa, bikin wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin a wurin yawon shakatawa na Ditan ya janyo hankulan masu yawon shakatawa masu tarin yawa daga sauran wuraren kasar Sin da kuma kasashen ketare domin sun iya kara fahimtarsu kan al'adun gargajiya na kasar Sin a zamanin yanzu. A cikin wannan kyakkyawan wurin yawon shakatawa, a tsakanin gine-ginen gargajiya na kasar Sin, musamman ma baki na iya ganin dimbin mutane da kayayyaki iri daban daban da abinci iri daban daban da kuma kallon harkokin al'adu masu ban sha'awa.'


1 2 3