Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-25 20:48:52    
Malam Guy Rufus Chambers, babban jami'i a babban kamfanin John Swire na kasar Birtaniya na kaunar birnin Xi'an

cri

A lokacin da yake zama a birnin Xi'an, Malam Guy Rufus Chambers ya ganam ma idonsa ci gaba da birnin Xi'an ya samu wajen bunkasa harkokinsa. A farkon lokacin zuwansa, gine-ginen birnin ba a zo a gani ba, hanyoyinsa ma matsattsu ne. Amma yanzu birnin ya riga ya sami manyan sauye-sauye. Alal misali, an gina manyan gine-gine iri na zamani birjika a cikin birnin, sabbin hanyoyin da aka shimfida ko fadada su suna yawa, yanzu kuma ana kara raya birnin cikin sauri. Malam Guy Rufus Chambers ya bayyana cewa, idan aka kalli waje daga ofishinsa, za a iya gano manyan injuna masu daukar kaya sama da 10 wadanda ke aiki don gina manyan gine-gine ba dare ba rana. A ganinsa, Xi'an tsohon babban birnin kasar Sin yana da makomarsa mai kyau. Ya kara da cewa, "birnin Xi'an yana da kyakkyawar makomarsa. Birnin ya kai matsayi na uku a cikin dukkan biranen kasar Sin wajen ba da ilmin jami'a, bayan birnin Beijing da na Shanghai. Haka kuma al'adun tarihi mas arziki na birnin tushe ne mai karfi ga raya birnin Xi'an."

Ko da yake Malam Guy Rufus Chambers yana kaunar birnin Xi'an sosai, amma zai tashi daga birnin nan gaba ba da dadewa ba. Babban kamfanin John Swire ya yanke shawara kan mayar da shi daga birnin Xi'an zuwa Hong Kong don ciyar da mukaminsa gaba. Malamin Guy Rufus Chambers yana ji ba ya son bar birnin. Ya ce, "na ji dadin zamana a birnin Xi'an har cikin shekaru biyu da suka wuce. Ina da aminai masu arziki da yawa a birnin. Amma na tabbata zan sami damar komawa birnin don aiki, in ba don aikina ba, tabbas ne, ni da iyalina za mu koma birnin a shekarar badi. Dalilin da ya sa haka shi ne domin birnin Xi'an wani birni ne na sigar musamman a fannin al'adu da tarihi da kayayyakin abinci masu dadin ci." (Halilu)


1 2