Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-02-25 20:48:52    
Malam Guy Rufus Chambers, babban jami'i a babban kamfanin John Swire na kasar Birtaniya na kaunar birnin Xi'an

cri

Malam Guy Rufus Chambers dan kasar Birtaniya ne, yana da shekaru 37 da haihuwa a bana. Yanzu shi babban manaja ne a kamfanin Coca ?Cola na babban kamfanin John Swire na kasar Birtaniya. Tun daga shekarar 1989, ya taba shafe shekaru hudu yana koyon Sinanci a Jami'ar Cambridge ta kasar Birtaniya. A lokacin da yake karatu a jami'ar, an taba aikawa da shi zuwa kasar Sin don zurfafa ilminsa na Sinanci a shahararriyar Jami'ar Jama'ar Kasar Sin.

Malam Guy Rufus Chambers ya ce, dalilan da suka sa ya yanke shawara kan koyon Sinanci a lokacin da yake karatu a jami'a shi ne domin bayan da ya karanta littattafai kan kasar Sin, ya gano cewa kasar Sin wata kasa ce mai girma da dogon tarihi. Kuma a wancan lokaci, kasar Sin ta riga ta shafe shekaru 10 tana aiwatar da manufar yin kwaskwarima da bude wa kasashen waje kofa, kuma tana bunkasa tattalin arzikinta cikin sauri. Bayan da ya gama karatunsa daga jami'ar, ya sami aikin yi a babban kafamnin John Swire. Kuma a shekarar 2005, an mayar da shi zuwa birnin Xi'an don kula da kamfanin cola-cola na wannan babban kamfani. Da malam Guy Rufus Chambers ya tabo magana a kan birnin Xi'an, sai ya ce, "birnin Xi'an birni ne mai girma sosai. Sanin kowa ne, a zamanin da, akwai daulolin gargajiya 13 wadanda suka mayar da birnin don ya zama babban birninsu na kasar Sin. Ban da wannan kuma birnin Xi'an yana da tarin abubuwa masu ban sha'awa."

Bayan da Malam Guy Rufus Chambers ya dade yana aiki da zama a birnin Xi'an, ya fahimci mazaunan birnin sosai. Ya kara da cewa, "mazaunan birnin Xi'an mutane ne masu gaskiya da kaunar baki sosai, don haka na daura abuta da su cikin sauki. Haka kuma baki 'yan kasashen ketare wadanda ke yin yawon shakatawa ko zama a birnin suna jin dadin wannan kwarai."

1 2